Okonjo-Iweala, da wasu ‘Yan takaran WTO 4 sun tsallaka zagaye na gaba

Okonjo-Iweala, da wasu ‘Yan takaran WTO 4 sun tsallaka zagaye na gaba

- An bar Ngozi Okonjo-Iweala a cikin masu neman shugabancin WTO

- Ragowar ‘Yan takarar 4 sun fito ne daga Saudi, Birtaniya da Koriya

- Amina Chawahir ta Kenya ce kadai ta rage daga Afrika bayan Iweala

Rahotanni sun fito daga Vanguard da Punch cewa kungiyar WTO ta cire sunayen wasu uku daga cikin ‘yan takarar da ke neman kujerar darekta-Janar.

Ana sa ran cewa kungiyar Duniyar za ta sake cire sunan mutum guda, yadda za a bar mutane biyu kadai su gwabza a takarar da za ayi nan da wasu kwanaki.

Abin farin cikin shi ne tsohuwar ministar tattalin arzikin kasar Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta na cikin wadanda aka bari a jeringiyar ‘yan takara.

Bloomberg ta fitar da rahoto a ranar 18 ga watan Satumba, 2020, cewa har yanzu Okonjo-Iweala ta na takarar.

KU KARANTA: ECOWAS za ta marawa tsohuwar Ministan Najeriya baya

Wadanda aka cire sunayensu sun hada da abokin hamayyar Ngozi Okonjo-Iweala a gida watau Hamid Mamdouh na kasar Masar.

Ragowar biyun da aka yi waje da su saboda rashin goyon-baya su ne Jesus Seade na kasar Mexico da kuma Tudor Ulianovschi, wanda ya fito daga kasar Moldoba.

Kungiyar WTO ta ce wadannan ‘yan takara uku da aka cire ba su samu isasshen goyon bayan da ake bukata a zagayen farko na zaben da aka shirya ba.

Shugaban majalisar WTO, David Walker, ya fitar da jawabi a ranar Juma’ar nan, ya ce kungiyar ta na daraja kowane daga cikin wadanda su ka shiga wannan takara.

KU KARANTA: Kasar Masar ta na so a hana Ngozi Okonjo-Iweala takara a WTO

Mista David Walker ya ke cewa duk masu neman wannan kujera, kwararrun mutane ne masu daraja.

Za a shiga zagaye na biyu na wannan zabe ne daga ranar 24 ga watan Satumba zuwa 6 ga watan Oktoba. Daga nan za a bar ‘yan takara biyu da za su fafata a karshe.

A baya kun ji Dr. Okonjo-Iweala ta bayyana burinta na neman wannan kujera ta sabon kungiyar kasuwancin Duniya da ke birnin Geneva da za a rantsar a Nuwamba.

Sauran masu takarar su ne Mohammad Maziad Al-Tuwaijri, Yoo Myung-hee, Amina Chawahir Mohamed Jibril. Dukkansu sun rike kujerun ministocin kudi ko kasuwanci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel