An naɗa Abba-Aji a Sakataren NEGF

An naɗa Abba-Aji a Sakataren NEGF

- Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, Farfesa Babagana Zulum ya nada Muhammad Abba-Aji a matsayin Sakatare na NEGF

- Kafin nadinsa Abba-Aji ya rike mukamin jami'in tuntuba na Majalisar Tarayya a lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Musa Yar'Adua da Goodluck Jonathan

- Nadin da aka yi wa Abba-Aji na tsawon shekaru biyu amma akwai yiwuwar sabuntawa idan akwai bukatar hakan kamar yadda sanarwar ta ce

An nada Abba-Aji a Sakataren NEGF
An nada Abba-Aji a Sakataren NEGF. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

An nada tsohon jami'in tuntuba na Majalisar Tarayya, Sanata Muhammad Abba-Aji a matsayin Sakataren kungiyar gwamnonin yankin Arewa ta Gabas, NEGF.

DUBA WANNAN: Hotuna: Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa

Abba-Aji ya rike mukamin jami'in tuntuba a majalisar tarayya a zamanin mulkin shugaban kasa Umaru Yar'adua da Goodluck Jonathan.

An fara nada shi mukamin na shekaru biyu sannan aka sabunta nadinsa kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mallam Isa Gusau, Kakakin gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum wanda shine shugaban kungiyar ya ce an sanar da nadin Abba-Aji ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watar 15 ga watan Satumban 2020 mai dauke da sa hannun Zulum.

KU KARANTA: Hotuna: Dan majalisar Najeriya sai aurar da ƴaƴansa 5 a rana ɗaya

Wani sashi na sanarwar ya ce, "Nadin da aka yi maka na shekaru biyu ne kuma ana iya sabunta nadin bayan karewar wa'adin. Za a tattauna da kai domin amincewa kan albashinka da sauran hakoki."

A wani rahoton, fitaccen mai kudin duniya kuma mai tallafawa al'umma Bill Gates ya yi magana game da matakan da Najeriya za ta iya dauka domin tsamo 'yan kasar daga talauci.

An yi kisayin cewa a kalla 'yan Najeriya miliyan 82.9 suke rayuwa cikin talauci, hakan yasa aka yi wa Najeriya lakabi "babban birnin talauci na duniya".

A wata hirar da The Cable ta yi da shi, an tambayi attajirin dan kasuwan hanyoyin da Najeriya za ta bi domin tsamo mutanen ta daga talauci, ya lissafa inganta kiwon lafiya, ingantaccen ilimi, karin haraji da sauransu.

Ya ce: "Ka san akwai hanyoyi mabanbanta da za a iya rage talauci. Wanda ya fi muhimmanci shine lafiya; idan yara suna girma cikin koshin lafiya za su iya samun ilimi su girma su bada gudunmawa a kasa, idan ka basu abinci mai kyau za su kara kuzari da hazaka."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel