Anambra: ‘Yan Sanda sun kama wanda ake zargi ya kashe tsohuwarsa

Anambra: ‘Yan Sanda sun kama wanda ake zargi ya kashe tsohuwarsa

- ‘Yan Sanda sun kama wanda ake zargi da laifin kashe mutane uku a Anambra

- Wannan mutumi ya kashe har da tsohuwarsa da kuma yaransa biyu da ya haifa

- Bayan haka wannan mutumi mai suna Emeka ya raunata ragowar ‘ya ‘yansa

Wani mummunan labari ya zo mana cewa an samu mutumin da ya bi cikin dare ya hallaka iyalinsa. Wannan ya faru ne a jihar Anambra.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa dakarun ‘yan sanda sun cafke Emeka Ezimadu da laifin hallaka mahaifiyarsa da kuma ‘ya ‘yansa.

Mista Emeka Ezimadu mai shekaru 47 ya aikata wannan laifi ne a karamar hukumar Nnewi.

Kamar yadda jami’an tsaron su ka bayyana, wannan tsohuwa mai shekaru 85 ta mutu ne a hannun ‘dan da haifa a ranar jiya Alhamis dinnan.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta ba 'yan kasa hakurin wahalar da ta ba su

‘Yan sanda sun ce Emeka Ezimadu ya yi amfani ne da adda, ya aukawa mahaifiyarsa da wasu ‘ya ‘yansa biyu a lokacin da su ke sharara barci.

Wannan mutumi asalinsa ‘dan garin Opuneze Uruagu da ke Nnewi, jihar Anambra. Bayan kashe mutum uku, ya raunata sauran ‘ya ‘yansa.

Ifechukwu mai shekara 9, da Mmeso ‘yar shekara 2 a Duniya sun gamu da ajalinsu ne a hannun mahaifinsu, wanda yanzu haka ya ke tsare.

Kakakin ‘yan sanda na jihar Anambra, SP Haruna Mohamed, ya ce wanda ake tuhumar ya raunta sauran ‘ya ‘yansa uku a harin daren yau.

KU KARANTA: Rikicin Gwamnati da Direbobi ta sa an daina dakon mai zuwa Arewa

Anambra: ‘Yan Sanda sun kama wanda ake zargi ya kashe tsohuwarsa
Emeka Ezimadu Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

An bada sunan ‘ya ‘yan da Mista Ezimadu ya yi wa rauni da Nonso, Chinaemerem, da Ngozi. Yaran sun a da shekaru 12, 11 da kuma 8.

Haruna Mohamed ya ce ‘yan sanda sun sheka da wadannan mutane zuwa asibiti, inda aka tabbatar da cewa yaran da kakarsu sun mutu.

Ragowar wanda aka yi wa rauni su na jinya a asibiti. Shi kuma wannan Bawan Allah ya na tsare a garin Awka, inda ake bincike a kansa.

Dazu kun ji cewa wani Ɗan majalisar tarayyar Najeriya, Honarabul Hassan Usman Sokadabo zai aurar da ƴaƴansa guda biyar duka a rana ɗaya.

Hassan Sokadabo ya wallafa katin gayyatar ɗaurin auren yaran na sa ne a kafofin sadarwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng