Logo: An ba Mai rike da kambun Barcelona, Messi dama ya yi amfani da tambarinsa

Logo: An ba Mai rike da kambun Barcelona, Messi dama ya yi amfani da tambarinsa

- Lionel Messi ya doke kamfanin Massia a shari’ar da Alkali kotun EU ya yi

- Babban kotun na Turai ya yi watsi da hukuncin da aka bada a kan Tauraron

- Messi ya samu damar ayi amfani da sunansa a kayan kamfanin kekekunan

Reuters ta ce shugaban ‘yan wasan kungiyar FC Barcelona da Argentina, Lionel Messi ya yi nasara a shari’ar da aka yi da shi da wani kamfanin kasar Sifen.

Kotu ta yanke hukunci cewa Lionel Messi ne mai cikakken iko a kan tambarinsa watau Logo.

Hakan na zuwa ne bayan wani babban kotun kungiyar kasashen Turai ya yi fatali da karar da aka kawo a kan shahararren ‘dan wasan na kasar Argentina.

Masu karar Lionel Messi sun daukaka kara ne zuwa kotun kungiyar EU da ke zama a kasar Luxembourg, amma ba su samu nasara a kan ‘dan wasan ba.

KU KARANTA: Kudin da Messi ya ke samu duk shekara a Barcelona

Wadanda su ke karar Messi; kamfanin Massi da kuma EUIPO na kungiyar kasashen Turai su na neman iko da tambarin ‘dan wasan mai shekaru 33 a Duniya.

A shekarar 2011 ne Messi ya rubutawa ofishin EUIPO takarda ya na bukatar su rika amfani da sunansa a jikin kayan wasanni da riguna da duk wasu kekunansu.

Kamfanin Massi masu hada kekuna sun nuna rashin amincewarsu game da wannan bukata, su ka ce amfani da sunan ‘dan wasan zai kawo masu rudani a kasuwa.

Logo: An ba Mai rike da kambun Barcelona, Messi dama ya yi amfani da takensa
'Dan wasa Lionel Messi
Source: Facebook

A karshe dai ofishin kungiyar kasashen Turai sun saurari kukan da kamfanin Massi su ka yi.

KU KARANTA: Mourinho ya na gab da doke Man Utd wajen sayen Bale

A shekarar 2013 ne aka yi watsi da karar da Messi ya daukaka, amma lauyoyin ‘dan wasan su ka sake kai maganar zuwa babban kotun kungiyar EU a 2018.

Bayan kusan shekaru biyu, Alkalan kotun da ke Luxembourg sun soke hukuncin da aka yi a baya, su ka ce ‘dan wasan ya na da gaskiya a kan kamfanin kekunan.

Kwanakin baya kun ji yadda ‘Dan wasan Tanis, Roger Federer ya zarce kaf 'yan wasannin Duniya har da irinsu Lionel Messi da Cristiano Ronaldo samun kudi.

Wadanda su ka biyo bayan Federer su ne Cristiano Ronaldo, Lionel Messi, da Neymar Jr.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel