Zaben Edo: Buhari ya fadawa jami'an tsaro da INEC yadda yake so a gudanar da zaben jihar

Zaben Edo: Buhari ya fadawa jami'an tsaro da INEC yadda yake so a gudanar da zaben jihar

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci jami’an tsaro da su yi aiki da hankali a lokacin zaben gwamnan Edo

- Shugaban Najeriyan ya bayar da shawarar ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai bashi shawara

- Buhari ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da yan takararsu da su bi ka’idojin damokradiyya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci jami’an tsaro da jami’an zabe da su kama mutuncin kansu a lokacin gudanar da zaben gwamnan jihar Edo.

Shugaban kasar ya bayar da shawarar ne a ranar Alhamis, 17 ga watan Satumba, a cikin wani jawabi ta hannaun kakakinsa, Garba Shehu.

Buhari ya kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa da yan takararsu da su bi tsarin damokradiyya a lokacin zaben.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: APC za ta kwashi kashinta a hannu idan aka cire ƴan bangar siyasa - Wike

Zaben Edo: Buhari ya fadawa jami'an tsaro da INEC yadda yake so a gudanar da zaben jihar
Zaben Edo: Buhari ya fadawa jami'an tsaro da INEC yadda yake so a gudanar da zaben jihar
Source: Twitter

Ya jaddada matsayarsa kan zaben gwamnan jihar Edo na ganin an yi shi cikin gaskiya da amana.

“Ina matukar kaunar zabe na gaskiya da amana, amma jajircewa na ni kadai ba zai isa ba idan sauran mutanen da abun ya shafa suka ki bin dokokin,” in ji Buhari.

Ya ce manufarsa na son ganin an daukaka damokradiyyar kasar zuwa babban mataki ba zai cimma nasara ba idan yan siyasa suka koma ga siyasar a mutu ko ayi rai.

Shugaban kasar ya bayyana siyasar ayi ko a mutu a matsayin barazana ga zabe na gaskiya da amana a kasar.

Ya bayyana cewa irin wannan tunani ya fi mayar da hankali ga nasara maimakon damuwa da sakamako na gaskiya wanda shine muradin mutane.

Buhari ya bayyana cewa jami’an tsaro da jami’an zabe su zamo a tsaka-tsaki.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Babban jigon APC ya yi hasashen nasara ga jam’iyyarsa

Ya roki dukkanin jam’iyyun siyasa da yan takararsu da su rungumi zaman lafiya a lokacin zaben.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Edo, ta yi godiya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan tura isassun tsaro zuwa jihar Edo, gabannin zaben gwamna na ranar 19 ga watan Satumba a jihar, jaridar Leadership ta ruwaito.

Babban sakataren labarai na jam’iyyar a jihar, Chris Osa Nehikhare, ne ya bayyana hakan a yayinda ya zanta da manema labarai a madadin kungiyar kamfen na PDP a Edo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel