Zaben Edo: Babban jigon APC ya yi hasashen nasara ga jam’iyyarsa

Zaben Edo: Babban jigon APC ya yi hasashen nasara ga jam’iyyarsa

- Wani jigon APC, Sam Nkire, ya yi hasashen nasara ga jam’iyyarsa a zaben gwamnan Edo mai zuwa

- Nkire ya yi ikirarin cewa hanya daya da PDP za ta bi tayi nasara shine yin magudin zabe

- Za a gudanar da zaben gwamnan jihar Edo a ranar Asabar, 19 ga watan Satumba

Yayinda yau saura yan kwanaki kadan kafin zaben gwamnan jihar Edo, wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Cif Sam Nkire, ya yi hasashen nasara ga jam’iyyarsa.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa Nkire wanda ya kasance mamba a kungiyar masu ruwa da tsaki na APC ta kasa, ya ce nasarar na iya zama gab da gab, inda ya kara da cewa ‘nasara sunansa nasara.'

Ya kuma ce wadanda ke ganin cewa har yanzu jihar Edo ta PDP ce toh suna a zamanin da ne, inda ya kara da cewa gwamnoni biyu na karshe a jihar duk yan APC ne.

KU KARANTA KUMA: Hujja ta yi ɓatan dabo: An samu tarnaƙi a shari'ar Fatima da Atiku Abubakar

Zaben Edo: Babban jigon APC ya yi hasashen nasara ga jam’iyyarsa
Zaben Edo: Babban jigon APC ya yi hasashen nasara ga jam’iyyarsa Hoto: Premium Times, Twitter/Osagie Oze-Iyamu
Asali: UGC

Nkire ya ci gaba da ikirarin cewa hanya guda da PDP za ta iya bi wajen yin nasara shine ta yin magudin zabe, idan ban da haka to lallai APC ce za ta yi nasara.

“A bayyane yake cewa ba halin jam’iyya mai mulki bane aiki da yan daba ko kuma kwace akwatin zabe, saboda haka, APC na bayar da tabbacin nasara mai tsafta ba tare da zamba ba,” in ji shi.

Ya jaddada cewa koda dai zaben gwamnan jihar Edo ba abun a mutu ko ayi rai bane ga APC kamar yadda yake ga PDP, jam’iyyarsa za ta sake jagorancin jihar Edo sau guda.

An shirya gudanar da zaben na jihar Edo a ranar Asabar, 19 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: PDP ta jinjinawa Buhari kan wani ƙoƙari da ya yi

Koda dai yan takara 14 ke neman kujerar, manyan yan takarar da aka fi mayar da hankali a kansu sune na APC, Osagie Ize-Iyamu da abokin adawarsa na PDP, Godwin Obaseki.

A wani labarin, babban jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi kira ga al'ummar jihar Edo suyi watsi da gwamna Godwin Obaseki, dake neman zarcewa kan kujerarsa.

A faifan bidiyon da tasahar TVC ta saki, Tinubu ya ce Obaseki ba jarumin demokradiyya bane kuma a yi waje da shi a zaben gwamnan ranar Asabar.

Tinubu na cikin jiga-jigan APC da suka yiwa Obaseki yakin neman zabe a shekarar 2016 karkashin jam'iyyar APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng