COVID-19: EU da Kasar Jafan sun ba Gwamnatin Kano gudumuwar $1.1m

COVID-19: EU da Kasar Jafan sun ba Gwamnatin Kano gudumuwar $1.1m

- Kungiyar EU ta ba Jihar Kano tallafin fiye da Naira miliya 400

- Wannan gudumuwa za ta taimaka wajen rage radadin COVID-19

- A baya Jihar Kano ya nemi agajin Naira biliyan 15 daga Buhari

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamnatin jihar Kano ta yi nasarar samun wasu makudan kudi a matsayin tallafin yaki da annobar cutar COVID-19.

Kungiyar kasashen Turai watau EU da kuma kasar Jafan ce su ka jihar Kano kudi da nufin rage radadin da Corornavirus ta jefa al’umma a shekarar nan.

Kamar yadda gwamnatin jihar Kano ta bayyana, kungiyar Turan da kasar waje ta aiko gudumuwar Dala miliyan 1.1 da za a taimakawa ‘yan kasuwa.

Wannan gudumuwa ta haura Naira miliyan 420 idan aka yi lissafinsu a kudin Najeriya.

KU KARANTA: Kasar Sin ta boyewa Duniya gaskiyar Coronavirus

Sanarwar nan ta fito ne dazu daga bakin sakataren yada labaran mai girma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje watau Malam Abba Anwar.

Abba Anwar ya ce an warewa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa wannan tallafi ne, kuma ana sa ran gudumuwar za ta taimaka wajen rage radadin da ake ciki.

Kamar yadda sakataren gwamnan ya bayyana a wani jawabi da ya fitar, mutane 1, 600 za su amfana da wannan kudi ta hanyar aikin karfi da za su yi a jihar.

Haka zalika akwai kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da su ke cikin tsarin SME fiye da 600 da ake harin za su amfana da gudumuwar dalolin da aka kawo.

KU KARANTA: Manyan mutanen da COVID-19 ta harba a Najeriya

COVID-19: EU da Kasar Jafan sun ba Gwamnatin Kano gudumuwar $1.1m
Buhari ya hana Kano tsabar kudi N15bn
Asali: UGC

Anwar ya ce tuni gwamna ya bada umarnin a zakulo wadanda su ka cancanta da wannan tallafi domin a agaza masu kamar yadda kungiyar EU ta gindaya sharadi.

Mai girma gwamna ya bada umarnin daukewa wadanda za su amfana kudin alhakin banki.

A baya gwamnatin Kano ta roki shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taimaka mata da kudi domin shawo kan COVID-19 a lokacin da annobar ta barke.

Gwamnatin tarayya ba ta ba gwamna Abdullahi Umar Ganduje wadannan kudi kamar yadda ya nema ba, amma ta bada gudumuwar kayan aiki da wasu tallafin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel