Aikin shaiɗan ne: Mutumin da ya kitsa sace maƙwabciyarsa da jaririnta ya magantu

Aikin shaiɗan ne: Mutumin da ya kitsa sace maƙwabciyarsa da jaririnta ya magantu

- Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta gurfanar da wani mutum mai suna Buba da ya kitsa sace makwabciyarsa da danta

- Buba ya ce sharrin shaidan ne ya kai shi ga aikata hakan domin shi bai san mutanen ba

- Ya ce wani makiyayi ne ya yaudaresa har ya yarda aka hada kai dashi bayan ya fada masa cewa za asamu miliyoyin kudi daga lamarin

Wani mutum mai suna Buba Mohammed wanda aka fi sani da Mallam, ya tona cewa ya hada kai da masu garkuwa da mutane daga Taraba da Adamawa domin sace makwabciyarsa Aishatu da danta mai watanni takwas.

Mohammed, wanda ya kasance amintaccen makwabci ga wani Aliyu Suleiman, mazaunin Yulde Pate, karamar hukumar Yola ta kudu, ya yi fallasan ne ga manema labarai a Yola.

Hakan ya kasance ne a lokacin da Kwamishinan yan sandan Adamawa, CP Olugbenga Adeyanju ya gurfanar dashi a hedkwatar rundunar a ranar Laraba, 16 ga watan Satumba.

A cewarsa, wani makiyayi mai suna Wakili ne ya tunkare shi da batun, cewa dan uwan Aliyu wani babban jami’in gwamnati a jihar zai biya miliyoyin naira a matsayin kudin fansa.

Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, Mohammed ya bayyana cewa shine ya tsara sannan ya sanar dasu halin da ake ciki lokacin tattauna batun kudin fansa.

Ya kuma shawarcesu da su yi garkuwa da matar da danta domin za su samu kudi mai yawa daga hakan shafin Linda Ikeji ta ruwaito.

Aikin shaiɗan ne: Mutumin da ya kitsa sace maƙwabciyarsa da jaririnta ya magantu
Aikin shaiɗan ne: Mutumin da ya kitsa sace maƙwabciyarsa da jaririnta ya magantu Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

Mohammed ya yarda cewa iyalan Aliyu na masa alkhairi sannan ya ce sharrin shaidan ne.

KU KARANTA KUMA: Hujja ta yi ɓatan dabo: An samu tarnaƙi a shari'ar Fatima da Atiku Abubakar

“Maganar gaskiya, ban san su ba kuma ban san Ina suka kai su ba. Abunda suka ce mun kawai shine za su bani kudi kuma N60,000 za su bani cikin miliyan 10 da suka karba a matsayin kudin fansa.

“Ina roko da ayi mani afuwa, sharrin shaidan ne, ban san me ya hau kaina ba,” ya fallasa.

Da yake bayyana halin da yake ciki, Aliyu Suleiman ya ce ya yi bakin cikin cewa Mohammed, wanda yake yi wa kallon makwabci nagari zai iya aikata haka ga iyalansa.

“Wannan mummunan al’amari da ya afku a ranar 11 ga watan Yulin 2020 ba zai taba gogewa daga zuciyana ba, masu garkuwa da mutanen sun kai farmaki gidana suna nema na,” in ji shi.

Suleiman ya tuna cewa a lokacin tattaunawa don sakin matarsa da dansa, masu garkuwan sun san abunda suka yanke shawarar yi a tsakaninsu tun kan su kira su.

“Daga wannan rana, na fahimci cewa yiwa mutane alkhairi babban laifi ne,” cewar shi.

KU KARANTA KUMA: Allahu Akbar: Yadda tsawa ta faɗa Taraba, ta kashe ƴan gida ɗaya su 3

A gefe guda, jama'ar kauyen Unguwar Gambo da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina sun kashe wasu 'yan bindiga wadanda da ba a san yawansu ba.

Wasu mazauna yankin sun sanar da jaridar Daily Trust cewa, lamarin ya auku a ranar Lahadi yayin da daya daga cikin wadanda ake zargin dan bindiga ne ya bayyana sunan wadanda suke hada kai wurin aika-aikar.

"Abinda ya faru shine, akwai wani mutum da aka yi garkuwa da dan sa kuma sai da ya biya kudin fansa ya karba dansa.

"Daga nan cikin kwanakin sai aka sake sace wani dan sa wanda jama'ar kauyen suka dinga addu'a tare da yanka domin neman taimakon Allah.

"A ranar Lahadi, wani mutum ya fito inda ya bayyana cewa yana daya daga cikin masu garkuwa da mutanen kuma ya sanar da sauran abokan aika-aikarsa. Daga nan ne jama'a suka damkesu tare da halaka su," in ji majiyar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel