Kaduna: Akwai masu dafa abincin bogi a shirin ba ‘Yan Makaranta abinci

Kaduna: Akwai masu dafa abincin bogi a shirin ba ‘Yan Makaranta abinci

- ActionAid ta ce akwai madafan bogi a tsarin raba abinci a Makarantu

- Gwamnatin Najeriya ta zo da wani shiri na ba ‘Yan makaranta abinci

- Kungiyar ta ce ta na binciken badakalar da aka tafka a jihar Kaduna

Kungiyar ActionAid Nigeria ta ce akwai sunayen masu dafa abinci na bogi da aka cusa a cikin tsarin ciyar da daliban makarantun gwamnati a Kaduna.

ActionAid Nigeria ta gano wannan ne a binciken da ta ke yi wa tsarin raba abinci ga yaran makarantun gwamnati da ke cikin kananan hukumomi 23 a jihar.

Wannan kungiya ta zo da wani shiri mai suna PATS-F domin yin binciken kwa-kwaf a jihar Kaduna.

Shugaban sashen aikin PATS-F na kungiyar ActionAid Nigeria ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa akwai madafa fiye da 7, 000 da su ke wannan aiki a jihar Kaduna.

KU KARANTA: Gwamnati ta ce ta ga tasirin rufe wasu gidajen karuwai a Kaduna

Mista Kehinde Arowosegbe ya ce ActionAid Nigeria za ta taimakawa gwamnatin jihar Kaduna wajen tankade da rairayar masu aikin gaskiya da kuma na bogi.

“Mun ga masu aikin bogi da-dama a cikin sunayen wadanda su ke dafa abinci, ba mu da cikakken adadinsu tukuna, har sai mun kammala nazarin alkalaumanmu.”

Kehinde Arowosegbe ya ce wannan ne karon farko da ake binciken aikin da gwamnatin ta shigo da shi.

A cewar Kehinde Arowosegbe, ActionAid Nigeria ta na son tantance ainihin yawan wadanda gwamnati ta dauka hayar dafawa yaran makaranta abincin kalaci.

KU KARANTA: Alhakin nemo Dadiyata ya na kan Gwamnan Kaduna - Kwankwasiyya

Kaduna: Akwai masu dafa abincin bogi a shirin ba ‘Yan Makaranta abinci
Gwamnan Kaduna tare da iyalinsa
Asali: Twitter

Arowosegbe ya ce sun yi shekara uku da kirkiro shirin PATS-F tare da hadin-kan kungiyoyi irinsu MacArthur Foundation, FOMWAN, NPTA, GCC da kuma CGC.

Gwamnatin Kaduna ce ta nemi ActionAid ta yi mata wannan aiki, domin ta gano gaskiyar yadda abubuwa su ke gudana. Yanzu an binciki makarantu sama da 400.

A makon jiya kuma kun ji yadda 'yan Majalisar dokokin Kaduna su ka yi na'am da a riƙa yi wa masu fyaɗe dandaƙar mazaƙuta saboda a daina lalata da yara.

‘Yan Majalisar sun yi wa dokokin fyaɗe garambawul, kuma gwamna ya rattaba hannunsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel