Allahu Akbar: Yadda tsawa ta faɗa Taraba, ta kashe ƴan gida ɗaya su 3

Allahu Akbar: Yadda tsawa ta faɗa Taraba, ta kashe ƴan gida ɗaya su 3

- Al’umman kauyen Pupule na jihar Taraba sun ga abun tashin hankali bayan tsawa ta fada kan wasu yan gida daya su uku da mahaifiyarsu

- A nan take yaran su uku suka mutu yayinda mahaifiyarsu ta ji munanan raunuka da yawa sakamakon konewa da tayi

- Iyalan na a hanyarsu ta dawowa daga gona ne lokacin da abun ya afku sakamakon ruwan sama mai karfi da aka yi

Tsawa ta fada kan wasu yan gida daya su uku inda ta yi sanadiyar mutuwarsu sannan ta kona mahaifiyarsu mai suna Justina Nyavoro a ranar Talata, 16 ga watan Satumba.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 5:30 na yamma a kauyen Pupule da ke karamar hukumar Yarro, lokacin da Justina da yaranta uku ke dawowa daga gona.

A cewar wata majiya a kauyen, matar da yaranta uku suna dawowa daga gona a yayinda ake ruwan sama mai karfi, da suka kusa da kauyen Pupule sai tsawar ta fada masu.

KU KARANTA KUMA: Hujja ta yi ɓatan dabo: An samu tarnaƙi a shari'ar Fatima da Atiku Abubakar

Allahu Akbar: Yadda tsawa ta faɗa Taraba, ta kashe ƴan gida ɗaya su 3
Allahu Akbar: Yadda tsawa ta faɗa Taraba, ta kashe ƴan gida ɗaya su 3 Hoto: Gettyimages/FBC News
Source: Getty Images

Majiyar ta ce yaran uku sun mutu a nan take yayinda mahaifiyarsu ta ji munanan raunuka da dama, an kwashe ta cikin gaggawa zuwa asibitin Pupule domin jinya.

Ta ci gaba da cewa an binne yaran su uku masu shekaru 12, 8 da 6 bayan yan sa’o’i kadan da afkuwar lamarin.

Wani sanannen mutum a kauyen kuma tsohon shugaban karamar hukumar Yorro, Mista Aicus Kovorova ya tabbatar da lamarin.

Ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki da radadi, ya kuma bayyana cewa mahaifiyar yaran na samun sauki.

A wani labari makamancin wannan, tsawa ta kashe mutum hudu cikin manoma biyar da suka fake a kasan bishiya yayin da ake tafka mamakon ruwan sama a kauyen Kukar-Gesa da ke karamar Katsina ta jihar Katsina.

Malam Musa Danladi, shugaban iyalan ya tabbatar da mutuwar 'ya'yansa biyu da jikansa daya kuma ya danganta hakan da hukuncin Ubangiji.

"Ruwan ya fara wurin karfe 5 na yamma a ranar Asabar, yayin da manoma biyar daga gidanmu suka je girbe geron daga gona," yace.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel