Jam’iyyar PDP ta na so a hana Gwamna Akeredolu da Ize-Iyamu barin Najeriya

Jam’iyyar PDP ta na so a hana Gwamna Akeredolu da Ize-Iyamu barin Najeriya

- PDP ta nemi kasashen waje su makawa Rotimi Akeredolu da Osagie Ize-Iyamu takunkumi

- Jam’iyyar adawar ta yi wannan kira ne a cikin makon nan

- Kola Ologbondiyan ya zargi Akeredolu da Ize-Iyamu da jawo tashin hankali a Edo da Ondo

Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta yi kira ga kasashen waje su sa takunkumin balaguro ga wasu daga cikin manyan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC.

PDP ta roki kasashen Duniya su hukunta gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu da ‘dan takarar APC a zaben jihar Edo watau Fasto Osagie Ize-Iyamu.

Jam’iyyar adawar ta na zargin Rotimi Akeredolu da Osagie Ize-Iyamu da laifin kawo rashin zaman lafiya.

KU KARANTA: An tsaida bizar Amurkar wasu masu magudin zabe a Najeriya

PDP ta nuna cewa ta na goyon bayan matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na haramtawa wasu ‘Yan Najeriya da aka samu da laifi shiga cikin kasarta.

Kola Ologbondiyan wanda shi ne sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP ya yi kira ga kasashen waje da su sa kafar wando daya da Osagie Ize-Iyamu da Rotimi Akeredolu.

Ologbondiyan ya zargi ‘dan takarar gwamnan APC a Edo, Osagie Ize-Iyamu, da laifin tada rikicin zabe.

Jam’iyyar PDP ta na so a hana Gwamna Akeredolu da Ize-Iyamu barin Najeriya
Gwamnan Edo Godwin Obaseki da Ize-Iyamu
Source: Facebook

Mai magana a madadin jam’iyyar PDP ya ce akwai hannun mai girma gwamna Rotimi Akeredolu a harin da aka kai wa ‘yan jam'iyyar PDP kwanan nan a jihar Ondo.

KU KARANTA: Jegede ya ce ana neman kashe shi, bayan an kai wa tawagarsa hari

Kasashen da ake so a haramtawa ‘yan siyasar shiga sun hada da UAE, Faransa, Sifen, Kanada da kuma sauran kasashen Afrika ta karkashin kungiyar ECOWAS.

Kamar yadda ku ka ji a baya, kasar Amurka ta sanya takunkumi a kan wadannan ‘yan siyasa ne sakamakon samunsu da aka yi da laifin tafka magudin zabe.

Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayarta a shafinta na Twitter a jawabinta na ranar Laraba.

A ranar Laraba, 16 ga watan Satumba, 2020, kakakin PDP na kasa, Kola Ologbondiyan, ya fitar da jawabi ya na yabon kokarin Amurka na ganin an yi zaben gaskiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel