PTD: Direbobin tankoki za su daina daukar mai daga Legas zuwa Yankin Arewa

PTD: Direbobin tankoki za su daina daukar mai daga Legas zuwa Yankin Arewa

- Akwai yiwuwar a shiga sabon wahalar mai saboda za a daina jigilar mai

- Gwamnatin Jihar Neja ta rufe hanyar Garin Minna domin ana gyaran titi

- Direbobin manyan motoci sun ce ba za su iya bin titin Bida – Lambata ba

A ranar Laraba, 16 ga watan Satumba, kungiyar PTD ta direbobin man fetur ta bada umarnin dakatar da jigilar mai daga Legas zuwa Arewacin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ce kungiyar direbobin manyan motan sun bayyana wannan ne a wani jawabi da su ka fitar ta bakin shugabansu na kasa, Salimon Oladiti.

Mista Salimon Oladiti ya bukaci ‘yan kungiyarsa ta PTD su daina aiki har sai baba-ta-gani.

A cewar Salimon Oladiti, wannan mataki da su ka dauka ya zama dole ne bayan gwamnatin jihar Neja ta haramtawa masu manyan motoci bi ta kan titunanta.

KU KATANTA: Akwai yiwuwar fetur ya kara tsada a Najeriya bayan karin darajar 2%

Gwamnatin Neja ta ce daga ranar 15 ga watan Satumban nan, babu wani mai babbar mota da za a bari ya hau kan titin garin Minna saboda wani aiki da ake yi.

Mai girma gwamna Abubakar Sani Bello da kansa ya rufe hanyar daga kan iyakar garin Bida a ranar Talata. Bello ya ce an yi haka ne domin a gyara wannan titi.

Amma kungiyar direbobin manyan motocin sun ce daga ranar Alhamis, ba za su dauko kaya daga Legas zuwa Arewa ba, domin an hana su ratsawa ta jihar Neja.

“Mota ba za ta iya bi ta kan titin da ya rage mana ba. Wannan shi ne titin Bida- Agai- Lapai- Lambata. Titin nan hanyar mutuwa ce.” Inji Salimon Oladiti.

KU KARANTA: Ana kokarin shigo mana da kaji masu COVID-19 - NCS

PTD: Direbobin tankoki za su daina daukar mai daga Legas zuwa Yankin Arewa
Direbobin tankoki sun yi yaji
Asali: Facebook

Shugaban PTD ya ce sun zauna da wani hadimin ministan ayyuka game da gyaran aikin Minna zuwa Bida bayan sun samu labarin shirin da gwamnatin Neja ta ke yi.

Mista Oladiti ya ce an yi masa alkawarin za a yi wani abu game da wannan hanya, amma makonni biyu kenan da yin maganar, babu abin da gwamnatin kasar ta iya yi.

Wannan na zuwa ne makonni kadan da yin karin farashin man fetur a Najeriya. Jam'iyyar hamayya ta nuna cewa ba ta goyon bayan wannan mataki da a aka dauka.

A dalilin karin kun ji cewa a Kaduna, ana kuka da yadda farashin motar haya ya tashi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel