Zaben edo: NSCDC ta tura jami’ai 13,311 da karnukan farauta 60

Zaben edo: NSCDC ta tura jami’ai 13,311 da karnukan farauta 60

- Rundunar tsaro ta Civil Defence ta ce ta tura kimanin jami’ai 13,311 zuwa jihar Edo

- Abdullahi Gana, shugaban NCDC ya ce an tura jami’an ne domin tabbatar da zabe na gaskiya da lumana

- Shugaban na NCDC ya kara da cewa an tura karnukan farauta 60 zuwa ofishin INEC domin kula da taron jama’a da kuma gano abubuwan fashewa

Gabannin zaben gwamnan Edo mai zuwa, hukumar tsaro na Civil Defence (NSCDC) ta tura jami’ai kimanin guda 13,311 zuwa jihar domin tabbatar da zaman lafiya.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa Abdullahi Gana, babban kwamandan NSCDC, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 16 ga watan Satumba, a Abuja.

Gana ya bayyana cewa an zabo jami’an da aka tura jihar ne daga hedkwatar rundunar da ofishoshinta na Kogi, Anambra, Bayelsa, Delta da kuma Ondo.

KU KARANTA KUMA: Mayaƙan Boko Haram sun kai sabon hari a Borno, mutane 8 sun mutu

Zaben edo: NSCDC ta tura jami’ai 13,311 da karnukan farauta 60
Zaben edo: NSCDC ta tura jami’ai 13,311 da karnukan farauta 60 Hoto: Thisday
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa hukumar tsaron ta kuma tura karnukan farauta da aka horar zuwa ofishin INEC domin kula da taron jama’a da kuma gano abubuwan fashewa da sauransu.

Shugaban na NCDC ya bayyana cewa an tura jami’an ne domin tabbatar da magance matsaloli na magudin zabe, rikici da sauran laifuka da ka iya shafar gudanarwar zaben.

Ya bayyana cewa an horar da dukkanin jami’an da aka tura a kan sabbin tsarin gudanawar zabe game da COVID-19 kafin tafiyarsu wajen aikin tsaron.

KU KARANTA KUMA: Garkame Omar Farouq saboda zargin ɓatanci ya saɓawa dokar mu - Saƙon UNICEF ga jihar Kano

A gefe guda, wani faifan bidiyo ya bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta wanda ke nuna masu yakin neman zabe suna amsan katin zabe mata suna basu turmin Atamfa.

Dubi ga irin hulunan da masu raba atamfofin suke sanye da su, ya nuna cewa suna 'POI' wanda ke nufin dan takaran jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Hakazalika daya daga cikin yan matan ta sanya dankwalin jam'iyyar APC.

Za'a gudanar da zaben jihar Edo ne ranar 19 ga Satumba, 2020.

Za a goge raini ne tsakanin gwamnan jihar, Godwin Obaseki, kuma dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, da Fasto Osaze Ize-Iyamu na jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel