Soji sun kai wa yaran Gana sumame a maɓuyarsu, sun kashe biyu sun kama 5
- Sojojin Najeriya na Operation Whirl Stroke sun kai sumamen maɓuyar tsohon shugaban masu tada ƙayan baya Gana da aka kashe a Benue
- Sunyi nasarar kashe ƴan tada ƙayan baya biyu sannan sun kama wasu biyar da ake zargin ƴan bindiga ne
- Sojojin sunyi arangama da wasu ƴan bindiga a maɓuyar sannan suka yi galaba a kansu suka kwato makamai da layu
Dakarun sojojin Najeriya a ranar Litinin sun lalata maɓuyar shugaban masu tayar da ƙayan baya na Benue da aka kashe Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana.
Sun kai sumammen ne a garin Adu da ke Chanchanji a ƙaramar hukumar Takum da ke jihar Taraba.
Sun kuma kashe masu tayar da ƙayan baya biyu sun kuma kama wasu biyar da ake zargin ƴan bindiga ne.
DUBA WANNAN: Bidiyo: Sojoji sun tarwatsa mafakan shugabannin 'yan bindiga Damina da Sani Mochoko a dajin Kuyambana a Zamfara
Wadanda aka kama sun hada da Saalu Terlumun, Benjamin Valentine da Milton Gbegi da aka kama a jihar Benue.
Sai kuma Isaac Hilega da aka yi wa lakabi da Bawasa da Godwin Terwase da aka kama a Chanchanji a jihar Taraba.
Sojojin sector 2 da aka girke a Gbise a ƙaramar hukumar Katsina-Ala na jihar Benue da sojojin sector 4 ne suka yi haɗin gwiwa suka kai sumamen da Adu.
A yayin sumamen, sojojin sun yi arangama da masu tada ƙayan baya da suka buɗe musu wuta a yayin da suka kusa isa maɓuyar.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mahaifi, sun yi awon gaba da ɗansa a Katsina
A cewar sanarwar da kakakin Hedkwatan Tsaro, John Enenche ya fitar, sojojin sun mayar wa ƴan tada ƙayar bayan wuta suka ci galaba a kansu hakan yasa suka tarwatsa da raunukan bindiga.
Kazalika, Sojojin sun kuma yi nasarar kwato bindigu ƙirar Pistol.
Sanarwar har ila yau ta ce Sojojin na Operation Whirl Stroke sun kwato wayoyin salula 16 da layu da wani ganye da ake zargi wiwi ne.
"Wadanda ake zargin suna amsa tambayoyi daga bisani za a mika su ga ƴan sanda domin cigaba da bincike. A halin yanzu sojoji sun mamaye unguwar suna sintiri domin hana miyagun saƙat," a cewar hedkwatar tsaro, DHQ.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng