Motocin kudin da ka kwamushe a gidanka ba za su iya siya maka Edo ba - Ikimi ga Tinubu

Motocin kudin da ka kwamushe a gidanka ba za su iya siya maka Edo ba - Ikimi ga Tinubu

- Tsohon ministan harkokin waje, Tom Ikimi ya caccaki Ahmed Bola Tinubu a yayin gangamin yakin neman zaben Obaseki da suka fita

- Ikimi ya ja kunnen Tinubu a kan cewa jiharE do ta fi karfinsa domin ba jihar Legas bace balle ya siyeta da kudaden da ya kwamushe a gidansa

- Ya kalubalanci Tinubu da ya fito ya bayyana tushen dukiyarsa domin kuwa a 1999 bashi da komai

Tsohon ministan harkokin waje, Tom Ikimi, ya sanar da babban jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu, cewa motocin da ke dankare da kudi a cikin gidansa ba za su iya siyan kujerar gwamnan jihar Edo ba a zaben da ke zuwa a ranar Asabar.

Ikimi ya sanar da hakan a gagarumin gangamin siyasa da 'yan jam'iyyar PDP suka fito a babban birnin jihar Edo a ranar Talata.

Tsohon ministan ya sanar da hakan ne yayin martani ga wani bidiyo wanda Tinubu yake kira ga jama'ar jihar Edo da kada su kuskura su zabi Obaseki.

A yayin martani ga bidiyon, Ikimi, wanda a da babban jigo ne a jam'iyyar APC, ya ce Tinubu bashi da wata dukiya a 1999 kafin ya hau kujerar gwamnan jihar Legas.

A don haka ya yi kira ga Tinubu da ya bayyana wa 'yan Najeriya tushen dukiyarsa.

Tsohon ministan, yayin magana a kan motocin kudin da aka gani a harabar gidan Tinubu a kusa da zaben 2019, ya ce ba zai yuwu a siya jihar Edo ba, kuma ya ja kunnen Tinubu da ya kiyayi jihar.

Ikimi ya ce bidiyon Tinubu wata babbar shaida ce da ke nuna cewa zaben ba tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da Fasto Osagie Ize-Iyamu bane kadai.

A maimakon hakan, zaben tsakanin Obaseki ne da Tinubu tare da Adams Oshiomhole.

A yayin jawabi, Ikimi ya ce, "Bola Tinubu, ka sanar da mu nawa gareka a 1999. A yau kai biloniya ne. Kana daukar kudi a manyan motoci domin gurgunta damokaradiyya.

KU KARANTA: Cikar Najeriya shekaru 60: Buhari ya kaddamar da sabon tambari (Hotuna da Bidiyo)

Motocin kudin da ka kwamushe a gidanka ba za su iya siya maka Edo ba - Ikimi ga Tinubu
Motocin kudin da ka kwamushe a gidanka ba za su iya siya maka Edo ba - Ikimi ga Tinubu. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

KU KARANTA: Kada ku karya tattalin arzikin Najeriya da korona - Majalisar dattawa

"Kana daukar kudade a motocin banki. Ina motocin kudin jihar Edo? Sun iso ne? Kudi ba zai iya siyan jihar Edo ba. Edo ba Legas bace."

Ikimi ya ce, yayin zaben fidda gwani na gwamnan jihar Legas, kowa na kaunar Akinwunmi Ambode amma banda Tinubu. Hakan yasa aka hana shi tikiti.

Tsohon minsitan ya ce duk da tausar Tinubu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dinga yi da sauran 'yan jam'iyyar, Tinubu ya ki sauraronsu.

A wani labari na daban, a ranar Talata, jam'iyyar PDP ta shawarci shugaban jam'iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu da ya shafa wa Godwin Obaseki, dan takarar Gwamnan jihar Edo, lafiya.

Ta shawarci Tinubu da ya fuskanci manyan makiyan da ke cikin jam'iyyar APC, Vanguard ta wallafa.

Tinubu ya ja kunnen jama'ar jihar Edo da kada su goyi bayan Obaseki domin bai cancanci a zabesa ba a matsayin shugaba.

A yayin martani ga bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani, PDP ta bakin sakataren yada labaranta, Kola Ologbondiyan, ya ce Tinubu ya saba dukkan dokokin damokaradiyya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel