Rufe gidajen mata da wuraren shan ruwa sun rage mana barna - Injiniya

Rufe gidajen mata da wuraren shan ruwa sun rage mana barna - Injiniya

- An rufe dakunan mata masu zaman kansu da gidajen ruwa a Sabon Gari

- Shugaban karamar hukumar Sabon Gari ya ce sun ga amfanin yin hakan

- A cewar Hon. Muhammad Usman, wannan ya sa masu laifuffuka sun ragu

Shugaban karamar hukumar Sabon Gari, jihar Kaduna, Hon. Muhammad Usman, ya yi magana game da matakan da ya dauka a kan gidajen tanbele.

Muhammad Usman ya ce rufe wuraren shan giya da neman mata da ke cikin yankin Sabon Gari a Zariya, ya yi sanadiyyar raguwar aikata laifuffuka.

Gwamnatin Muhammad Usman wanda aka fi sani da Injiniya, ta kawo dokoki da su ka canza yadda ake mu’amala da kayan ruwa a karamar hukumar.

Kwanakin baya majalisa ta amince da dokokin da su ka kafa sharudan sha da saida kayan maye.

KU KARANTA: Gwamnati ta garkame haramtattun dakunan caca – Hukumar KADRIS

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnati ta shiga rufe duk wasu gidajen mata da wuraren shan giya da ke cikin bainar jama’a bayan an kawo wannan sabuwar doka.

Masu wannan sana’a sun kai gwamnatin karamar hukumar kotu, amma babban kotun tarayya da ke garin Dogarawwa, ya yi fatali da karar da su ka shigar.

Usman ya ce a Yunin 2020, majalisa ta shigo da wannan doka ta takaita amfani da kayan maye kamar yadda sashe na hudu na kudin tsarin mulki ya tanada.

Haka zalika Hon. Usman ya ce dokar kananan hukumomi ta uku ta shekarar 2018, ta ba majalisarsa damar kawo wannan doka da za ta yi tasiri kan cinikin giya.

Wannan doka da aka sa wa hannu a 2020 ta ba gwamnatin karamar hukumar damar kula da yadda ake talla, adana, da raba kayan basara a cikin yankin Sabon Gari.

KU KARANTA: Kudin fetur: Gwamnatin Tarayya za ta yi zama da ‘Yan kwadago

Rufe gidajen mata da wuraren shan ruwa sun rage mana barna - Injiniya
Alhaji Muhammad Usman Hoto: NNN
Source: Facebook

A cewar shugaban karamar hukumar, an samu raguwar laifuffuka bayan shigowar wannnan doka.

“Mafi yawan mazauna su na jin dadin abin da majalisar ta yi.”

“Babu wani tashin hankali ko matsin lamba game da dokar.”

“Masu saida giya a yankin su na aiki ne ba tare da lasisi ba, kamar yadda doka ta tanada.”

A makon nan ne Legit.ng Hausa ta rahoto cewa gwamnati ta bada umarnin rufe wasu wuraren caca a jihar Kaduna saboda rashin samun cikakkiyar rajista.

Shugaban KADIRS ya ce su na bin kamfanoni irinsu Bet9ja, KingBet da Derby Lotto bashin haraji

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel