‘Yan Sanda sun kama mutanen da ake zargi da fashi da satar mutane a Adamawa

‘Yan Sanda sun kama mutanen da ake zargi da fashi da satar mutane a Adamawa

- ‘Yan Sanda sun kama mutane 36 da ake zargi da aikata laifuffuka a Adamawa

- Ana zargin wadannan mutane da fashi da makami da kuma garkuwa da jama’a

- Kwamishinan ‘Yan Sanda ne ya gabatar da su a gaban ‘yan jarida a makon nan

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa jami’an ‘yan sanda na jihar Adamawa sun gurfanar da wasu mutane da ake zargin masu laifi ne a gaban jama’a.

Ana zargin wadanda aka cafken da laifuffukan da su ka hada da fashi da makami, da fyade, da kuma garkuwa da mutane domin samun kudin fansa.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa, CP Olugbenga Adeyanju ya gabatar da wadannan mutane har su 36 a gaban ‘yan jarida a garin Yola.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun tura Dakaru na musamman domin shirya zaben Edo

Kwamishinan ya jinjinawa kokarin jami’an da su ka yi nasarar cafke wadanda ake zargi da laifin, ya kuma yaba da goyon bayan da su ke samu daga sauran jama'a..

Ya ce: “An ci wannan nasara ne a dalilin namijin kokari da sadaukar da kai da jajirtattun dakarunmu da sauran rundunar shiyyar nan su ka yi.”

Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa: “Da kuma goyon baya sosai da ake samu daga gwamnati da mutanen kirkin jihar Adamawa.”

Olugbenga Adeyanju ya ce sun karbe bindigogi samfurin AK 47 da G3 da kuma casbi 199 na harsashi da wasu alburusai daga hannun wadannan miyagu.

KU KARANTA: Jami’an DSS su na neman Mahadi Shehu bayan ya yi wasu kalamai

‘Yan Sanda sun kama mutane da ake zargi da fashi da satar mutane a Adamawa
Gwamnan Adamawa, Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri Hoto: Today.ng
Asali: Facebook

Bayan haka, CP Olugbenga Adeyanju ya ce sun samesu da makudan kudi da wata motar gona.

Rundunar ‘yan sanda ta bada satifiket din jinjina ga wasu mazauna jihar, a dalilin rawar da su ke takawa da kuma gudumuwar da su ke ba jami’an tsaro.

Idan mu ka koma bangaren gidan soja, za mu labarin yadda jaruntar Janar Lamidi Adeosun ta yi wa Janar Tukur Buratai rana a lokacin farkamakin Boko Haram.

Shugaban hafsun sojin kasar, Tukur Buratai, ya ce mataimakinsa ya taba ceton ransa a 2015.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel