Jam’iyyar APC ta fara shirye-shiryen ladabtar da Ojudu, da wasu mutane 12

Jam’iyyar APC ta fara shirye-shiryen ladabtar da Ojudu, da wasu mutane 12

- APC za ta dauki mataki a kan wadanda su ka nunawa Jam’iyya kunnen-kashi

- Ana zargin wasu ‘Ya ‘yan jam’iyya a Jihar Ekiti da laifin sabawa umarnin NEC

- Elder Sam Oluwalana ya ce wadanda za a ladabtar sun hada da Babafemi Ojudu

A ranar Talatar nan ne jam’iyyar APC mai mulki ta kafa wani kwamitin mutum takwas da aka ba alhakin ladabtar da wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyya.

APC ta reshen jihar Ekiti ta na zargin wasu ‘ya ‘yanta da sabawa umarnin da majalisar koli ta jam’iyya watau NEC ta yi, don haka ta yi tanadin hukuntasu.

Darektan hulda da yada labarai na APC a Ekiti, Elder Sam Oluwalana, ya ce tsohon kakakin majalisar dokoki¸ Patrick Ajigbolamu zai jagoranci kwamitin.

Elder Sam Oluwalana ya bayyana cewa jam’iyya ta yi wannan ne bisa umarnin majalisar NEC.

KU KARANTA: Jiga-jigan PDP a Jihar Ekiti su na rikici

Jaridar Punch ta rahoto Elder Oluwalana ya na cewa: “Idan za ku tuna, a ranar 25 ga watan Yuni, 2020, NEC ta dauki matakin cewa ka da wasu ‘ya ‘yan jam’iyya su cigaba da shigar da kara a kotu.”

Ya ce, “An umarci kowa ya janye karar da ya kai, domin a shawo kan rikicin cikin gidan jam’iyya.”

A cewarsa, NEC ba ta goyon bayan sabanin da ake samu, don haka ta dauki wannan mataki, kuma ta bada umarnin ladabtar da wadanda su ka saba wannan umarni.

Darektan yada labaran na APC ya ce wannan kwamiti da aka kafa zai kammala aikinsa ne cikin kwanaki 19, sannan ya gabatar da rahoto a gaban uwar jam’iyya.

KU KARANTA: COVID-19 ta hada-kan Ayo Fayose da Gwamna Kayode Fayemi a Ekiti

Jam’iyyar APC ta fara shirye-shiryen ladabtar da Ojudu, da wasu mutane 12
Fayemi ya na samun sabani da Ojudu Hoto: APC
Asali: UGC

Wadanda ake zargi da sabawa umarnin da NEC ta bada sun hada da hadimin shugaban kasa, Sanata Babafemi Ojudu, Ayo Ajibade; da kuma Femi Adeleye inji Oluwalana.

Sauran su ne: Tsohon ‘dan takarar gwamna a Ekiti, Dr. Wole Oluyede; surukin jagoran jam’iyya Bola Tinubu watau Oyetunde Ojo, Bunmi Ogunleye da Dele Afolabi.

Ragowar wadanda kwamitin zai zauna a kansu su ne: Cif Akin Akomolafe; Bamigboye Adegoroye; Olusoga Owoeye; Toyin Oluwasola, da kuma Ben Oguntuase.

A jiya kun ji cewa tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya ajiye sabaninsa da Obasanjo, ya taya shi yi wa Gwamnatin APC ta shugaba Muhammadu Buhari kaca-kaca

Tsohon Gwamnan ya ce duk da ba ya tare da Obasanjo, babu shakka Gwamnatin Buhari ta gaza.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng