Haraji: KADIRS ta bayyana abin da ya sa hukuma ta ke rufe wuraren wasan caca

Haraji: KADIRS ta bayyana abin da ya sa hukuma ta ke rufe wuraren wasan caca

- Gwamnatin Kaduna ta rufe shaguna da-dama da ake yin wasan caca

- KADIRS ta ce wadannan shaguna sun sabawa dokar haraji ta Kaduna

- Ana bin kamfanonin Bet9ja, KingBet da kuma Derby Lotto bashin haraji

Hukumar KADIRS mai alhakin tattara haraji ta bayyana cewa ta rufe wuraren wasan caca da ke jihar Kaduna wadanda ba ayi wa rajista ba.

KADRIS ta yi wannan bayani ne ta bakin shugaban sashen wasanni, Mista Liye Anthony.

Liye Anthony ya shaidawa ‘yan jarida a wata hira cewa KADIRS ta rufe duk dakunan cacan da gwamnatin jihar Kaduna ba ta san da zamansu ba.

Anthony ya ce sun fara wannan aiki ne a Ranar Alhamis da ta gabata, kawo yanzu sun rufe wurare 13 da mutane su ke yin caca ba tare da bin doka ba.

Jami’an KADIRS sun rufe ofisoshi goma na kamfanin Bet9ja da KingBet. Bet9ja da KingBet su na cikin manyan kamfanonin caca da su ka shahara.

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa ta ci mutane da-dama a Bauchi

Haka zalika an rufe ofisoshi biyu na kamfanin Access Bet. Ofishin karshe da aka rufe a jihar kamar yadda Liye Anthony ya bayyana shi ne na Derby Lotto.

A dokar haraji da aka yi wa garambawul ta shekarar 2020 ta jihar Kaduna, an wajabtawa kamfanoni yin rajista da samun lasisi kafin su fara aiki.

Jami’in KADRIS ya bayyana abin da ya sa hukuma ta rufe wuraren wasan caca
Shugaban KADIRS. Dr. Zaid Abubakar Hoto: VON
Source: Facebook

Wadannan kamfanoni na caca sun saba wannan doka, inda su ka bude shaguna a fadin jihar ba tare da sun samu takardun izni daga hukumar KADIRS ba.

Sashe na 86 na dokar haraji ya farlantawa irin wadannan kamfanoni biyan N400, 000 a matsayin kudin rajista, daga nan ne gwamnati ta ke bada lasisin aiki.

KU KARANTA: Kudin da ake kashewa duk wanda ya kamu da Coronavirus a Kaduna

Bugu da kari sashe na 91 na dokar ya wajabta biyan 10% na ribar da aka samu ta caca a karshen kowane wata, mafi yawan kamfanoni ba su bin wannan doka.

Binciken da KADIRS ta yi ya nuna cewa akwai sama da shagunan caca 1500 da ke aiki a Kaduna ba tare da sun samu takardun rajista da lasisin fara aiki ba.

Gwamnati ta ce za ta cigaba da rufe haramtattun shaguna. Shugaban KADIRS, Zaid Abubakar, ya ce ana bin kamfanonin bashin haraji na kusan Naira miliyan 500.

A makon jiya ne Majalisar Kaduna ta amince da dokar dandaƙa ga masu fyaɗe. ‘Yan Majalisar sun yi wa dokokin fyaɗe garambawul ne a wani zama da su ka yi.

Kamar yadda ku ka ji, abin da ba a sani ba shi ne hukuncin da aka tanada ga mata masu fyade.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel