Najeriya ta na neman zaba abin da ta zama a karkashin Shugaba Buhari inji Ayo Fayose

Najeriya ta na neman zaba abin da ta zama a karkashin Shugaba Buhari inji Ayo Fayose

- Ayodele Fayose ya ce ya yarda da abin da Obasanjo ya fada a kan mulkin APC

- Tsohon Gwamnan ya ce Obasanjo ya yi gaskiya da ya soki Gwamnatin Buhari

- Fayose duk da irin banbancinsa da tsohon Shugaban ya yi tarayya da shi a nan

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Peter Fayose, ya ce ya yarda da abin da Olusegun Obasanjo ya fada game da halin da Najeriya ta ke ciki a halin yanzu.

Ayodele Fayose ya na ganin cewa tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi gaskiya.

Jagoran jam’iyyar PDP, Ayo Fayose ya bayyana haka ne a lokacin da ya yi wata hira kai tsaye da shugaban kamfanin Ovation Media Group, Dele Momodu.

An yi wannan hira da fitaccen ‘dan adawar ne a ranar 12 ga watan Satumba, 2020, ta shafin Instagram. Fayose ya na cikin manyan ‘yan adawar Buhari.

Fayose ya ke cewa ko da ya ke ba a cika samun jituwa tsakaninsa da Obasanjo a kan harkokin kasa ba, babu shakka abin da ya fada a kan gwamnatin APC gaskiya ne.

KU KARANTA: Obasanjo ya jikawa Buhari aiki - Balarabe Musa

Gawurtaccen ‘dan siyasar ya ke cewa a cikin hirar da aka yi da shi cewa abubuwan da ya fada game da Muhammadu Buhari a 2015, duk sun bayyana a fili.

Fayose ya ce babu wata gaba ta mutum-da-mutum tsakaninsa da Buhari, ya ce sabaninsu ta siyasa ce a dalilin rashin tsaro da tulin bashin da ya ke karbowa kasa.

“Duk cikin tsofaffin shugabannin kasa, ba ni son Obasanjo, zan fada maka gaskiya; Ba na son hanyoyinsa ko kadan. Ba na kan shafi guda tare da shi.” Inji Fayose.

Najeriya ta na neman zaba abin da ta zama a karkashin Shugaba Buhari inji Ayo Fayose
Ayo Fayose Hoto: Vanguard
Source: UGC

“Amma Obasanjo shi kadai ne shugaban kasar da ya taimaki Najeriya a nan da can.”

Daga cikin alheran Obasanjo inji Fayose shi ne ya adanawa Najeriya kudi. "Game da abin da ya fada yau (Asabar), ka iya cewa na yarda da shi, a nan dai na yi na’am."

KU KARANTA: Obasanjo ya sake sukar Buhari

“Lokacin da na fara magana a kan Buhari, har kai Dele Momodu ka soke ni. Yanzu mafi yawanku, ku na cikin jin kunya.”

“Duk abin da na fada sun tabbata.”

“Na fada a 2015, shugaba Buhari zai zama shingen barayi wajen sace kudin kasar nan. Na fadi wannan, na ce ba zai iya rike kasar nan ba."

“Shekaru biyar na APC, sun fi 16 da PDP ta yi muni.”

Olusegun Obasanjo ya ce abubuwa sun kama hanyar sukurkucewa a kasar nan, a karkashin gwamnatin APC da Muhammadu Buhari ya ke jagoranta.

A ra’ayin Fayose, APC ta jefa kasa cikin matsala. Hadimin shugaban kasa Buhari, Malam Garba Shehu da ACF sun maidawa Obasanjo raddi bayan ya soki mai gidansa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel