Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda 4

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda 4

- Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade a ma’aikatar tarayya

- Sabbin nade-nade sune na baya-bayan nan da aka yi a hukumar ma’aikatar tarayya

- Shugaban kasar ya nada sakatarorin dindindin guda hudu a ranar Litinin, 14 ga watan Satumba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nada sabbin sakatarorin dindindin guda hudu a hukumar ma’aikatan tarayya.

Dr Folashade Yemi-Esan, shugabar ma’aikatan tarayya ce ta bayyana hakan a wani jawabi da aka saki a ranar Litinin a Abuja.

Daraktan labarai na ofishin shugabar ma’aikatan, Olawunmi Ogunmosunle ce ta fitar da sanarwar, Daiy Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya tarar da barna a kasa, amma ya kara tabarbarar da abubuwa, in ji Balarabe Musa

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda 4

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda 4 Hoto: Daily Nigerian
Source: UGC

Wadanda aka nada sune Sule James daga jihar Kaduna, Abubakar Ismaila daga jihar Kebbi, Misis Patricia Robert daga jihar Kebbi da kuma Shehu Shinkafi daga jihar Zamfara.

A cewar Misis Yemi-Esan, za a sanar da lokacin rantsar dasu idan lokaci yayi.

A wani labari na daban, mun ji a cewa a ranar Talata, 2 ga watan Yuni, 2020, majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da Dr. Muheeba Farida Dankaka a matsayin shugabar hukumar raba dai-dai ta kasa watau FCC.

Majalisa ta amince da mukamin da shugaban kasa ya ba Farida Dankaka da wasu mutane 36 a hukumar da ke da alhakin ganin an yi adalci wajen raba arzikin kasa da mukami.

KU KARANTA KUMA: Bude boda: Ku ci abinda kuka shuka - Sakon Buhari ga ƴan Nigeria

‘Yan majalisar kasar sun yi na’am da wannan mataki ne bayan sun yi la’akari da wani rahoto da shugaban kwamitin da ke lura da aikin hukumar, Danjuma La’ah ya gabatar.

Bisa dukkan alamu kwamitin sanata Danjuma La’ah mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a karkashin PDP ya yi na’am da wadannan nadin mukamai da shugaban kasar yayi.

A ranar 18 ga watan Maris, 2020, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikowa majalisar dattawa takarda, ya na neman a tabbatar masa da nadin wadannan mutane a FCC.

Wannan zabi da fadar shugaban kasa ta yi ya jawo ce-ce-ku-ce inda wasu su ka nuna adawar su da zaben Muheeba Farida Dankaka da aka yi a matsayin sabuwar shugabar hukumar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel