Babu tilasci: Jagoran ƴan bindiga ya miƙa wuya a Katsina, ya ba da bindiga AK47 guda 3

Babu tilasci: Jagoran ƴan bindiga ya miƙa wuya a Katsina, ya ba da bindiga AK47 guda 3

- Kasurgumin dan bindiga Sada ya shiga hannun rundunar soji a Katsina

- Sada da kanshi ne ya mika wuya a sansanin sojin da ke Dansadau

- Ya kuma mika wa rundunar bindigogin Ak 47 uku, bindiga mai jigida da kuma mujalla

Wani shahararren dan bindiga da aka fi sani da suna ‘Sada’, ya mika kansa ga rundunar soji a sansaninsu da ke Dansadau sannan ya mika masu bindigogin AK 47 guda uku, bindiga mai jigida da mujalla biyu.

Mukaddashin daraktan labarai na ayyukan soji, Birgediya Janar Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan ga manema labarai a babban sansani na 4 a Faskari, jihar Katsina.

Ya ce mika wuyan da dan bindigan yayi ya kasance sakamakon matsin lamba daga Operation Sahel Sanity, jaridar The Nation ta ruwaito.

A wani aikin kuma, rundunar da ke gudanar da aikin bincike a hanyar Bingi sun kama wani da ake zargin dan bindiga ne, Isah Shehu.

KU KARANTA KUMA: Bude boda: Ku ci abinda kuka shuka - Sakon Buhari ga ƴan Nigeria

An kama shi ne dauke da kayan sojoji a cikin wata jaka.

Babu tilasci: Jagoran ƴan bindiga ya miƙa wuya a Katsina, ya ba da bindiga AK47 guda 3

Babu tilasci: Jagoran ƴan bindiga ya miƙa wuya a Katsina, ya ba da bindiga AK47 guda 3 Hoto: Vanguard
Source: Twitter

Bincike ya nuna cewa ya kasance wani kasurgumin dan fashi da mambobin kungiyarsa ke ma lakabi da ‘Kwamanda’.

A cewar Onyeuko, dan bindigan na tsare yanzu haka inda yake ba sojoji muhimman bayanai.

Ya ce: “A kokarin kakkabe yan bindiga da duk wasu miyagu a yankin arewa maso yamma, rundunar Operation Sahel Sanity sun kara rubanya kokarinsu kan haka. Hazikan sojin sun yi gagarumin nasara a kan yan bindiga da sauran miyagu a yankin.

“A ranar 30 ga watan Agusta 2020, bayan sun samu bayanai abun dogaro kan shige da ficen yan bindiga dauke da dabobbi 40 na sata a yankin Kwanar Maje, dakarun sojin sun yi gaggawan zuwa wajen sannan suka kama yan bindigar a hanyar Anka-Gummi. Sai dai suna hango sojin daga nesa, sai yan bindigar suka zubar da dabobbin sannan suka tsere cikin daji. An yi nasarar kwato dukkanin dabobbin sannan a mika wa masu shi.”

Ya kuma bayyana cewa rundunar da aka tura Faskari a jihar Katsina domin aikin sintiri sun gamu da wasu yan bindiga tare da wasu mata biyu da suka sato.

Ya kara da cewa bayan musayar wuta mai zafi, yan bindigan sun yasar da matan biyu wadanda aka mika su ga yan uwansu.

KU KARANTA KUMA: Ya kamata ka sani, ƴan Nigeria na shan bakar wahala - Jega ya aikawa Buhari sako

An yi musayar wuta da yan bindiga a Mararaban Kawaye bayan wani bayani da aka samu cewa yan bindiga sun sace wasu matafiya uku.

Sojijin sun yi nasarar gano su sannan suka fafata da su wanda hakan ya tursasa yan bindigan guduwa su bar mutanen da suka sace a jeji.

A wani labarin kuma, a kokarin ganin bayan 'yan bindiga da suka addabi yankin arewa maso yamma, rundunar Operation Sahel Sanity, ta ceto mutum 32 da aka yi garkuwa da su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel