Buhari ya tarar da barna a kasa, amma ya kara tabarbarar da abubuwa, in ji Balarabe Musa

Buhari ya tarar da barna a kasa, amma ya kara tabarbarar da abubuwa, in ji Balarabe Musa

- Furucin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kan gwamnatin Buhari na ci gaba da kawo cece-kuce

- Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa, ya shiga sahun masu sharhi kan lamarin

- Musa ya ce da hannun Obasanjo cikin halin da kasar ke ciki a yanzu, amma ya kara da cewar Buhari ya kara tabarbarar da lamarin

Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa, ya ce tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayar da gudunmawa wajen saka Najeriya a halin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya risketa na tabarbarewa.

Jigon kasar na martani ne ga furucin da Obasanjo ya yi a kwanan nan game da gwamnatin Buhari.

Tsohon shugaban Najeriyan ya caccaki Shugaba Muhammadu Buhari, kan yanda yake tafiyar da harkokin kasar, inda ya yi gargadin cewa Najeriya na lalacewa cikin sauri a karkashin mulkin Shugaba Buhari.

KU KARANTA KUMA: Jerin jihohi 28 da za su fuskanci ruwan sama mai tsanani kafin karshen 2020

Obasanjo ya yi ikirarin ne a lokacin gabatar da wani jawabi a wani taron sasanci da aka yi a Abuja, babbar birnin tarayya.

Buhari ya tarar da barna a kasa, amma ya kara tabarbarar da abubuwa, in ji Balarabe Musa
Buhari ya tarar da barna a kasa, amma ya kara tabarbarar da abubuwa, in ji Balarabe Musa Hoto: BBC
Asali: UGC

Alhaji Musa ya ce da ace Shugaba Obasanjo da wadanda suka gabace shi sun yi kokari, da Najeriya bata tsinci kanta a mummunan halin da take ciki ba a yanzu.

“Da ace ya yi abunda ya kamata sannan wadanda suka gabace shi sun yi abunda ya kamata, da lamarin bai yi wa Buhari muni ba,” ya fada ma jaridar Daily Trust a wata hira.

A cewarsa, dukkanin shugabannin da suka gabata musamman wadanda suka yi mulki kafin shugaba Obasanjo da wadanda suka yi a bayansa sun gazawa kasar.

Ya kara da cewa shugaba Buhari wanda ke shan wahalar rubabben tsarin ya kara tabarbarar da ita.

Kalamansa: “Mu kasance masu fadawa kanmu gaskiya saboda mun san su kuma mun girmi wasun su.

“Mu fadi gaskiya a yanzu da muke raye. Kuma gaskiyar magana shine duk sun gaza daya bayan daya.

KU KARANTA KUMA: Farashin kayan abinci ya fadi warwas a jihar Taraba, a Kano, Katsina, Benue da Nasarawa abun babu sauki

“Wadanda suka gabata sun lalata lamuran; Buhari wanda ya zo a baya-bayan nan, ya kara tabarbarar da lamarin.

“Ko mai Buhari zai yi, ba zai iya daidaita lamarin ba sai Allah ne kadai zai iya chanja komai.”

A baya mun ji cewa , Olusegun Obasanjo ya sake sukar Shugaba Muhammadu Buhari inda ya ce ƙasar ta kama hanyar lalacewa kuma kawunnan yan kasar sun rabu.

Obasanjo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a wurin wani taron da kungiyoyi masu wakiltan yankunan kasar suka hallarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel