Zaben gwamna: Ganduje ya yi wa Edo tsinke, ya tara al’umman Hausawa domin su zabi Ize-Iyamu
- Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa jihar Edo tsinke domin yi wa dan takarar gwamna na APC, Osagie Ize-Iyamu kamfen
- Ganduje ya tara al'umman Hausawa mazauna Edo inda ya bukaci da su zabi Ize-Iyamu a zaben ranar Asabar mai zuwa
- Gwamnan ya jadadda cewa zabar dan takarar APC daidai yake da zabar Muhammadu Buhari
Gwamnan jihar Kano kuma shugaban kungiyar kamfen din jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben Edo, Abdullahi Umar Ganduje da tawagarsa sun ziyarci al’umman Hausawa da ke Eyaen, wajen birnin Benin.
Ganduje ya bukaci da su zabi APC a zaben gwamnan jihar da za a yi a ranar Asabar mai zuwa.
Da yake jawabi ga taron Hausawa, Ganduje ya ce zabar APC tamkar zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari ne da kuma goyon bayansa wajen ci gaba da gyara Najeriya.
A nashi bangaren, tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole ya ce Ize-Iyamu zai ci gaba da ayyukan da gwamnatinsa ta fara wanda yace Gwamna Godwin Obaseki ya ci gaba dasu.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sace yan gida daya su 17 a Kaduna
Da yake jawabi ga dandazon jama’an, Ize-Iyamu ya ce zai yi amfani da ajanda mai sauki wajen dawo da farin ciki a zukatan mutanen jihar.
A fadar Enogie na Eyaen, mai martaba Osazuwa Idurase, a Edo, Ganduje ya ce: “Mun zo tattara yan uwanmu na arewa mazauna nan domin su zabi APC da Fasto Osagie Ize-Iyamu a zaben ranar Asabar mai zuwa.
“Mun san cewa sarakunanmu na gargajiya ba yan siyasa bane amma sune iyayenmu dukka don haka muka zo ayi mana addu’a domin mu cimma manufarmu. Mun san rawar ganin da majalisar sarakuna ke takawa wajen daidaita kasar.”
KU KARANTA KUMA: Farashin kayan abinci ya fadi warwas a jihar Taraba, a Kano, Katsina, Benue da Nasarawa abun babu sauki
A nashi bangaren, Idurase ya ce: “al’umman Hausawa sun dade a nan kuma suna samun tsaro yadda ya kamata, sun kasance yan cikinmu. Allah zai amsa addua’armu na zaman lafiya da tsaro."
A wani labarin kuma, Gwamna Godwin Obaseki da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, sun kaddamar da sansanin Alhazai a Benin, babbar birnin jihar Edo.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng