Matar Alaafin Aishat ta ce mijinta ya fi matasa da dama iya tarairayan mace

Matar Alaafin Aishat ta ce mijinta ya fi matasa da dama iya tarairayan mace

- Daya daga cikin matan Alaafin na Oyo, Aishat Folashade Adeyemi, ta bayyana cewa mijinta ya iya tarairayan mata

- Da take magana a kansa, ta ce koda yaushe ya kan aika direbansa ya kai mata abinci a lokacin da take makaranta

- Sarauniyar ta kara da cewa wasu lokutan ma ya kan taimaka mata wajen girki

Aishat Folashade Adeyemi, daya daga cikin matan Alaafin na Oyo, Lamidi Adeyemi, ta sake jan hankalin kafafen sadarwa yayinda ta jinjinawa angonta mai shekaru 84.

A wata hira da jaridar The Nation, Folashade ta bayyana cewa ta hadu da mijin nata, wato sarkin a lokacin da ta je yawon bude ido a fadarsa.

A lokacin tana da shekaru 25 a duniya, ta kara da cewa babu mamaki yanayinta na yawan tambaya ne ya janye hankalin sarkin zuwa wajenta.

Matar Alaafin Aishat ta ce mijinta ya fi matasa da dama iya tarairayar mace
Matar Alaafin Aishat ta ce mijinta ya fi matasa da dama iya tarairayar mace Hoto: Instagram/Folashade
Asali: Instagram

Da aka tambaye ya kan martanin iyayenta a lokacin, ta bayyana cewa koda dai da fari mahaifiyarta ta dan tsorata, ko daya abun bai damu mahaifinta ba.

KU KARANTA KUMA: Kwankwaso ya kaddamar da sansanin Alhazai a Edo

Folashade ta kara da cewa Alaafin ya kasance mutum da ya iya soyayya, inda ta kara da cewa wasu lokutan ya kan aika direbansa ya kai mata abinci lokacin da take makaranta.

Ta jadadda cewa basaraken ya fi matasa da dama iya tarairayan mace.

“Sarki ya kasance mutum da ya iya soyayya sosai. Idan baka kusa dashi, ba za ka san yana da kula da alkhairi ba. Wasu lokutan idan ina a madafi, zai zo ya taimaka mani. Lokacin da nake makaranta, zai turo direbansa da abinci ya kawo mani makaranta.

"Akwai tazarar shekaru sosai a tsakaninmu amma hakan baya haka shi nuna mani kauna. Yana nuna soyayya fiye da wasu matasan da kuke gani a waje. Abunda matashi zai iya yi, sarki na yin fiye da hakan,” in ji ta.

Ta bayyana cewa auren babban basaraken kasar Yarbawa bai tauye mata komai ba a rayuwa domin ta yi abubuwa da dama kamar gama makaranta, yin kasuwanci da kuma burin tafiya kasar wajen yin digiri na biyu.

KU KARANTA KUMA: Farashin kayan abinci ya fadi warwas a jihar Taraba, a Kano, Katsina, Benue da Nasarawa abun babu sauki

A baya mun kawo maku cewa Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi II, ya bayyana cewa wasu abubuwa game da yadda ya auri matansa masu jini a jika.

A cewar sarkin wanda aka fi sani da Iku Baba yeye, bai tsara auran mata da yawa ba. Ya bayyana cewa duk sune suke kawo kansu.

Ya bayyana cewa bayan ya taimaki matansa ta hanyar tura su makaranta, sai su yanke shawarar kin tafiya maimakon haka sai su zabi zama da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng