Farashin kayan abinci ya fadi warwas a jihar Taraba, a Kano, Katsina, Benue da Nasarawa abun babu sauki
- Farashin kayan abinci ya fadi warwas a yankunan kauyuka jihar Taraba
- Hakan ya kasance ne saboda billowar sabbin hatsi da manoma suka gibe
- A jihohin Kano, Katsina, Benue da Nasarawa abun babu sauki, har yanzu farashin na sama
An samu raguwar farashin kayayyakin abinci a yankunan karkara da ke jihar Taraba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Yankunan da aka samu karyewar farashin kayayyakin sun hada da Mutum Biyu, Garba Chede, Maihula, Dakka, Garbabi, Tella Monkin da kuma Jatau.
An tattaro cewa a yanzu ana sayar da masara sabuwar girbi a kan farashin N8000 a kasuwar Maihula yayin da farashinta ya ke kan N7000 a Dakka.
Hakazalika a kasuwannin Mutum Biyu da kauyan Garba-Chede, ana sayar da buhun masara sabuwar girbi a tsakanin N12,000 da N11,000.
KU KARANTA KUMA: Dubi kyawawan hotunan kasaitaccen biki na kannen uwargidar gwamnan jihar Kogi
An kuma gano cewa, ana sayar da 100kg na masara tsohuwar ajiya a tsakanin farashin N13,000 zuwa N15,000 a kasuwannin kauyukan da ke fadin jihar.
Karyewar farashin kayan hatsin na zuwa ne a yayin da manoma a fadin jihar ke ci gaba da girbi bayan samun amfanin gona.
Farashin sabuwar shinkafa ‘yar gida ya sauko daga N17,000 kan kowani buhun 100kg inda a yanzu ake sayar da duk buhu guda a kan N12,000.
A yanzu dai ana sayar da duk kwano daya na shinkafa ‘yar gida a kan N900 sabanin yadda aka rika siyarwa a kan N1,200 a makon da ya gabata.
KU KARANTA KUMA: Atiku ya yi ta’aziyya ga Sanata Wamakko kan mutuwar ‘yarsa
Sauran kayan abinci da suka hada da doya, rogo, wake da kuma gyada duk sun fado kasa.
Wani manomi, Alhaji Ali Maihula ya bayyana cewa, saukin farashin kayan abincin da ake samu a yanzu na da nasaba ne da yadda manoma suke samun karin yabanya da kuma albarka ta amfanin gona da suke girbewa a bana.
Ya ce a hakan ma farashin kayan abincin ya fi sauki a yankunan karkara da suke fuskantar kalubale wajen fito da amfanin gonakinsu sakamakon rashin hanya mai kyau.
Farashin kayayyakin na ci gaba da tashi a Kano, Benue, Nasarawa da Katsina
Binciken farashin kayayyaki a Kano ya nuna cewa a kasuwar hatsi na Dawau, ana siyar da buhun 100kg na shinkafar Jamila kan N54,000.
Har ila yau ana siyar da buhun 100kg na wake kan N21,000.
Haka kuma, ana siyar da buhun 100kg na tsohuwar masara kan N22,000 sannan ana siyar da sabuwar masara kan N18,500
Buhun 100kg na gero na tafiya kan N20,000 yayinda 100kg na garri ke kan N18,500.
An kuma tattaro cewa an samu kari kan kayan gona domin ana siyar da matsakaicin doya kan N650.
A cewar Malam Sagir Bello, wani mazaunin jihar ya ce: “Mutane da dama sun koma siyan karyayyun shinkafa wanda shine na karshe a gyararriyar shinkafa kuma dun da haka, ana siyar da mudu kan N550 a baya amma a yanzu ta kai N950 sannan mudun masara N600 ake siyar da ita yanzu.”
Rahotanni daga jihar Benue ya nuna cewa ana siyar da buhun Semobita kan N3,600, buhun shinkafa yar gida 50kg kan N25,000 yayinda yar waje kuma ke a kan N31,000.
Ana siyar da buhun filawa 50kg an N13,500, yayinda 100kg na garri ke a kan N26,000.
Daga jihar Katsina wani rahoto ya nuna cewa ana siyar da buhun 100kg na sabuwar masara kan N13,000, yayinda ake siyar da tsohuwar ajiya kan N19,000 buhun sabuwar wake N18,000, tsohuwa kuma N20,000.
A kasuwar Akwanga da ke jihar Nasarawa, ana siyar da buhun 50kg na shinkafa yar waje kan N32,000 yayinda na gida ke kan N28,000 sannan buhun filawa kuma na a kan N13,400.
10kg na Semobita na a tsakanin N3,600 da N4,000.
A wani labarin kuma, Ibrahim Gambari, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce tashin farashin kayayyakin abinci na ɗan ƙaramin lokaci ne.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng