Wasu mutum 30 sun kai wa yan sanda hari, sun kashe guda sun datse hannun guda

Wasu mutum 30 sun kai wa yan sanda hari, sun kashe guda sun datse hannun guda

- Wasu gungun miyagu su 30 sun afka wa jami'an ƴan sanda a jihar Abia sun kashe guda sun datse hannun guda

- Miyagun sun kuma sace bindigu ƙirar Ak-47 da alburusai daga hannun yan sandan bayan kai musu hari

- Rundunar yan sandan ta ce ta kama mutum huɗu da ke da hannu a harin kuma suna taimaka wa rundunar don gano sauran

Yan sanda a jihar Abia sun kama mutum huɗu da ake zargi da hannu wurin kisar wani sufetan yan sanda mai suna Princewill Divine.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Misis Janet Agbede ce ta bayyana hakan yayin jawabin da ta yi wa manema labarai a ranar Juma'a a Umuahia kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wasu mutum 30 sun kai wa yan sanda hari, sun kashe guda sun datse hannun guda

Wasu mutum 30 sun kai wa yan sanda hari, sun kashe guda sun datse hannun guda. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

Agbede ta ce marigayi Divine yana cikin yan sanda squadron 28 da 55 da wasu suka kai wa hari a ranar 7 ga watan Satumba a Okagwe junction, Ohafia.

Ta ce wasu ƴan bindiga 30 da har yanzu ba a gano ko su wanene bane suka afka wa yan sandan a yayin da suka fake wa ruwan sama.

Agbede tace: "Miyagun dauke da bindigu da adduna da wasu makamai sun mamayi ƴan sandan suka harbi ɗaya kuma suka sari ɗaya da adda.

"Ɗaya daga cikin yan sandan, Princewill Divine ya mutu nan take, ɗaya an datse masa hannu sannan sauran sun jikkata."

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa ƴar Sanata Wamakko rasuwa a Sokoto

Ta ce miyagun sun kuma sace bindigan AK-47 guda uku da alburusai daga hannun yan sandan duk da cewa akwai yiwuwar suma sun samu rauni.

Kwamishinan ta ce an kama mutum huɗu da ake zargi suna da hannu cikin kai harin kuma suna taimaka wa rundunar don gano sauran.

Agbede ta yi kira ga likitoci, ma'aikatan lafiya da masu magungunan gargajiya da ke jihar da wajen jihar su sanar da rundunar idan wasu sun taho wurinsu da raunukan harsashi.

A wani labarin daban, kun ji cewa, Rundunar Ƴan sandan jihar Katsina sun kama wani hatsabibin mai garkuwa da mutane, Abubakar Ibrahim a dajin Rugu da ke jihar.

An kuma ceto mutum uku da ya yi garkuwa da su bayan kama mai garkuwa da ake zargin yana cikin ƙungiyar masu satar mutane da ke adabar mutane a ƙananan hukumomin Batsari, Safana, Ɗan Musa da Kurfi a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel