Tashin gobara a ofishinmu na Ondo ba zai hana zaben gwamnan jihar ba – INEC

Tashin gobara a ofishinmu na Ondo ba zai hana zaben gwamnan jihar ba – INEC

- Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi martani a kan gobarar da ya afku a ofishinta da ke Ondo

- INEC ta bayyana cewa bata da masaniya kan abunda ya haddasa gobarar wacce ta lakume na'urorin Card Reader da yawa

- Sai dai ta bayar da tabbacin cewa hakan ba zai shafi zaben gwamnan jihar da ke gabatowa ba

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa har yanzu bata gano makasudin afkuwar gobarar da ta kona kwantena biyu da ta zuba na'urorin Card Reader guda 5,141 ba a inda aka ajiye su a ofishinta a Akure.

Ta ce lamarin ba zai shafi gudanarwar zaben gwamnan jihar da za a yi ba a ranar 10 ga watan Oktoba.

Hukumar zaben ta bayar da tabbacin cewa ba za a dage zaben gwamnan ba, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kwamishinan zabe na jihar Ondo, Rufus Akeju, ya ce gobarar ta fara ne bayan ma’aikatan hukumar sun tashi aiki a wannan rana.

Tashin gobara a ofishinmu na Ondo ba zai hana zaben gwamnan jihar ba – INEC Hoto: Hukumar zabe
Tashin gobara a ofishinmu na Ondo ba zai hana zaben gwamnan jihar ba – INEC
Asali: Twitter

Akeju ya ce an yi duk shirye-shiryen da ya kamata domin maye na'urorin Card Reader da suka kone da wasu.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa Buhari: Noma shi ne mafita ga matasa masu jini a jika

Ya jinjinawa hukumar kashe gobara kan hana annobar yaduwa zuwa sauran bangarorin ofishin.

Kwamishinan zaben na Ondo ya ce hukumar ta fara rabon kayayyaki yayinda ta fara yi wa jami’an tsaro horo na musamman domin basu damar mayar da hankali kan aikin a ranar zabe.

Gwamna Oluwarotimi Akeredolu, wanda ya sha alwashin ba hukumar gudunmawa ta kowani bangare da ya dace ya ce jihar Ondo na tsumayin ranar 10 ga watan Oktoba.

A baya mun ji cewa ofishin hukumar gudanar da zaben kasa mai zaman kanta INEC dake Akure, birnin jihar Ondo na ci bal-bal yanzu haka.

Hukumar INEC ta bayyana cewa gobarar ta lalata kayayyakin zabe. Hakazalika ba'a san abinda ya haddasa gobarar ba har yanzu.

KU KARANTA KUMA: Wasu yan iska na shirya yadda wani tsohon gwamna zai gaji Buhari - Kabiru Marafa

Wannan gobara na zuwa ne saura wata daya zaben gwamnan jihar da aka shirya ranar 10 ga watan Oktoba, 2020.

A jawabin da kakakin hukumar, Barista Festus Okoye, ya saki, ya ce wutar ta kona kwantenan da aka ajiye na'u'rorin Card Reader. Ya ce za'a kaddamar da bincike ba tare da bata lokaci ba idan aka kammala kashe wutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng