Tattalin arziki: Gumi, Yabo, Jingir, da sauran Malaman da su ke so ta sake zani

Tattalin arziki: Gumi, Yabo, Jingir, da sauran Malaman da su ke so ta sake zani

- Ana fama da matsanancin tsadar rayuwa a Najeriya a daidai wannan lokaci

- Gwamnatin Tarayya ta yi sabon karin kudin shan wutar lantarki da man fetur

- Malamai sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya duba halin da ake ciki

A cikin watan Satumban nan ne gwamnatin Najeriya ta yi sabon karin farashin man fetur, bayan haka kuma kudin shan wutar lantarki ya tashi a wurare da-dama.

Bugu da kari ana fama da matsanancin tashin kayan abinci da mutane su ka dogara da su. Wannan ya sa ta kai malamai, sun fara fitowa su na fadakar da hukuma.

Ga kadan daga cikin wadanda su ka yi magana game da halin da al’umma su ka shiga:

KU KARANTA: Masu 'Sai Baba' duk munafukai ne inji Shehi

1. Ahmad Gumi

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya tattauna da BBC Hausa a ranar Talata inda ya soki tsarin gwamnatin APC na rufe iyakokin kasa, ya ce wannan ya jawo mutane su ke fuskantar tsadar kayan abinci.

2. Lawal Shuaibu Abubakar

Lawal Shuaibu Abubakar wanda aka fi sani da ‘Malam Lawal Triumph’ a wani darasi ya roki gwamnatin tarayya ta saukaka talakawa a halin da ake ciki, malamin ya yi kuka da ya ke wannan jawabi.

3. Nasidi Goron-dutse

Sheikh Nasidi Abubakar Goron-dutse ya na cikin wadanda su ke wayyo Allah da yanayin da jama’a su ke ciki. Babban malamin ya ce tun da ya ke bai taba ganin al’umma su na wahala irin yanzu ba.

KU KARANTA: Babu dalilin kara farashin fetur da kudin wuta - Gumi

4. Bello Yabo

Sheikh Bello Yabo ya soki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a dalilin tsadar kayan abinci da farashin man fetur. Yabo a wani karatu da ya ke yi, ya ce gwamnatin APC ta gaza, har gara mulkin baya.

Tattalin arziki: Gumi, Yabo, Jingir, da sauran Malaman da su ke so ta sake zani

Bala Lau tare da Shugaban kasa Hoto: JIBWIS
Source: Twitter

5. Sani Yahaya Jingir

Dattijon malamin nan na kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana cewa duk da shekarunsa kusan 70 a Duniya, bai taba jin labarin irin tsadar da kayan abinci su ka yi a halin yanzu ba.

KU KARANTA: Bello Sokoto: Irinsu Isa Pantami su ka fi dacewa da shugabanci

Legit.ng Hausa ta samu labarin cewa limamin masallacin ITN da ke garin Zariya, jihar Kaduna, Dr. Mustapha Isa Qasim ya yi kira ga shugabanni su zama masu tausayin jama’a.

Mustapha Qasim a hudubar Juma’a ta yau, ya koka da matsalar tsaro, rashin kyawun hanyoyi, da tsadar kayan masarufi, ya ce akwai bukatar masu mulki su tausaya talakawa.

Shi kuwa Dr. Saeed Yunus ya yi kira ga jama’a su komawa Ubangiji domin samun sauki.

A baya kun ji cewa Sheikh Murtala Bello Sokoto ya yi kaca-kaca da gwamnatin Shugaba Buhari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel