Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta gamsu a sake bude makarantun boko ba

Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta gamsu a sake bude makarantun boko ba

- Da alamu har yanzu babu tabbacin bude makarantun boko a fadin Najeriya

- Ministan ilmi, Chukwuemeka Nwajiuba ya nuna rashin shirin gwamnati

- Chukwuemeka Nwajiuba ya ce za a iya daukar COVID-19 a wajen karatu

Babu mamaki yara da malamai za su cigaba da zaman gida domin kuwa har yanzu babu tabbacin gwamnatin tarayya ta shirya bada umarnin bude makarantu.

Hakan na zuwa ne bayan wani jawabi da karamin ministan ilmi na kasa ya yi a ranar Alhamis.

A ranar 10 ga watan Satumba, 2020, Honarabul Chukwuemeka Nwajiuba ya yi zaman kwamitin shugaban kasa da ke yaki da annobar COVID-19 a birnin tarayya Abuja.

Kwamitin PTF sun gana da majalisar NTLC ta sarakunan gargajiyan Arewacin Najeriya, inda aka tatttauna game da halin da ake ciki da kuma shirin komawa karatu.

KU KARANTA: Babu ranar komawa aji yanzu - Minista

Ministan ya ce har yanzu gwamnati ta na duba yiwuwar bude makarantu domin a koma bakin aiki, kawo yanzu gwamnati ba ta kammala wannan nazari da ta ke yi ba.

Jaridar The Nation ta ce Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana wannan ne a lokacin da Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III ya jefa masa tambaya jiya.

Sa’ad Abubakar III ya bukaci jin ta bakin gwamnati game da lokacin da yara za su koma aji.

“A yanzu ba mu cin ma matsayar da za mu ce mun gamsu makarantu za su iya daukar nauyin kansu, don haka a bude a cikin kwanciyar hankali.” Inji Ministan.

KU KARANTA: Kungiya ta bukaci a tsige Ministan ilmi Adamu Adamu

Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta gamsu a sake bude makarantun boko ba
Yaran Makaraanta a Jihar Oyo Hoto: Legit
Asali: Original

Karamin Ministan ya kara da: “Tawagarmu ta fita, ta zagaya, kuma za mu yi amfani da gaba daya wannan makon da kuma mako mai zuwa wajen karantar lamarin.”

Chukwuemeka Nwajiuba ya ce ma’aikatar ilmi za ta duba yadda ake bin dokoki da matakan da hukuma su ka gindaya a wuraren daukar karatu kafin a bude makarantu.

Rahoton ya ce mai girma ministan ya kafa hujja da abin da masana su ka fada a baya na cewa za a iya kamuwa da cutar COVID-19 a makarantu wajen daukar darasi.

Kwanaki kun ji cewa Gwamnati ta fara zama domin tsara yadda ‘Dalibai za su koma makaranta ba tare da zama cikin hadarin kamuwa da cutar Coronavirus ba

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel