Dr. Jonathan ya ce amfani da na’urar zamani ce hanyar gudanar da zabe nagari

Dr. Jonathan ya ce amfani da na’urar zamani ce hanyar gudanar da zabe nagari

- Dr. Goodluck Jonathan ya na kira a koma yin zabe da na’urorin zamani

- Tsohon Shugaban ya ce ta haka ne za a san ana damukaradiyya a Afrika

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, ya yi magana game da yadda za a rika gudanar da zabe mai inganci a Najeriya da sauran kasashen Afrika.

Dr. Goodluck Jonathan ya bayyana cewa amfani da na’urar zamani wajen shirya zabe ne kawai dabarar da za a bi domin gujewa magudi da murdiyar zabe a Nahiyar.

Yayin da ya ke jawabi a wajen wani shiri mai suna Ihe Osasu Show Symposium 2020, tsohon shugaban ya bada shawarar gudanar da zabe na gari a yankin Afrika.

Goodluck Jonathan ya ke cewa ta hanyar kada kuri’a ya kamata a rika fito da shugabanni – Ba kotu ba.

KU KARANTA: Jonathan ya ci amanar PDP a zaben 2019 - Kungiya

“A wurina idan har musamman Afrika ta na son ta cigaba, ba maganar yawan shirya zabe ba ne kawai, mu na da kasashe 15 a yankin yammacin Afrika, a bana kurum akwai zabuka 5.”

Har wa yau, Jonathan ya ce abin tambayar ita ce: “Saboda haka wajen gudanar da zabuka, mu na samun cigaba, amma wadannan zaben su na da inganci?”

Tsohon shugaban Najeriyar ya nuna alamar tambaya game da kyawun zaben da ake shiryawa a kasashen Afrika, ya ce abin da ake so shi ne burin talakawa ya yi tasiri.

“Zabe a kan kari abu ne mai kyau, amma zabe ba shi kadai ba ne damukaradiyya. Idan kuri’un mutanen kasa ba su aiki, babu bambanci da mulkin soji.” Inji Jonathan.

KU KARANTA: Fitaccen Mawaki Rarara ya ce ya daina yi wa Buhari waka har sai an biya kudi

Dr. Jonathan ya ce amfani da na’urar zamani ce hanyar gudanar da zabe nagari
Ebele Jonathan da Buhari Hoto: Fadar Shugaban kasa
Source: Twitter

Ya ce: “Saboda haka abin da za a fara gyarawa shi ne ganin yadda kuri’a za ta tsaida shugaba.”

Dr. Jonathan ya cigaba da jawabi, ‘Duba da yadda ake shirya zabe a Nahiyar nan, akalla daga zabukan da na sa-ido, abin da na gani shi ne dole mu shigo da tsarin zabe ta na’ura.”

“Mutane za su iya jin cewa za a iya yin murdiya, wasu kwararrun miyagu za su iya kutsawa cikin na’urar su yi wasu abubuwa, amma duk da haka, ana aiki da na’urori wajen aika miliyoyin Dalolin kudi a Duniya.”

Shugaban ya ce: “Don haka ina ganin cewa wannan ce mafita gaskiya.”

Jonathan ya yi mulki tsakanin 2010 zuwa 2015, ya rasa mulki ne bayan ya sha kasa a hannun APC. Muhammadu Buhari ya yabe shi a lokacin da bayan zaben 2019.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel