Shugaban kasa ya fadawa Gwamnan CBN ka da a saki kudin shigo da taki da abinci

Shugaban kasa ya fadawa Gwamnan CBN ka da a saki kudin shigo da taki da abinci

- Gwamnatin Muhammadu Buhari ta na nan a kan bakarta na hana shigo da abinci

- Shugaban kasar ya fadawa babban banki cewa ka da a ba kowa kudin kawo abinci

- Gwamnatin APC ta na kiran a koma gona domin kasar ta samu abincin da za ta ci

Masu shigo da takin zamani da kayan abinci cikin Najeriya daga kasashen ketare ba za su samu kudin kasar waje daga hannun CBN domin kasuwancinsu ba.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kara bada umarni ga gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emiefile, cewa ka da a fitar da kudi da nufin shigo da abinci.

Mai girma shugaban kasar ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da kwamitin NFSC da aka kafa domin ganin Najeriya ta samu isasshen abin da za a ci.

Idan ba ku manta ba an yi wannan zama ne a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, 10 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Rarara ya ce ya daina yi wa Buhari waka sai an aika masa N1000

Bayanin wannan umarni ya fito ne daga bakin Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Garba Shehu, wanda ya ce shugaban kasar ya jaddada matsayarsa.

Malam Garba Shehu ya ce Muhammadu Buhari ya tabbatar da umarnin da ya taba badawa da fatar baki na cewa babu wanda za a ba kudi ya shigo da abinci Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da tsarin ESP wanda daga cikin kudirorin wannan tsari shi ne Najeriya ta noma abin da za ta ci, sannan a samar da aiki ta harkar gona.

Da ya ke bayani game da rawar da gwamnatinsa ta taka wajen bunkasa harkar gona, Buhari ya ce, ‘Daga wuraren hada takin zamani 3, yanzu akwai 33 da ke aiki.”

KU KARANTA: Fadar Shugaban kasa ta yi magana game da tsadar kayan abinci

Shugaban kasa ya fadawa Gwamnan CBN ka da a saki kudin shigo da taki da abinci
Shugaban kasa da Gwamnan CBN Hoto: PUNCH
Source: UGC

Muhammadu Buhari ya ce: “Ba za mu fitar da ko sisin kobo daga asusun kudin kasar wajenmu domin a shigo da takin zamani ba. Za mu karfafa mutanenmu na gida.”

Bayan haka, shugaban kasar ya bada umarni a rika mikawa gwamnonin jihohi taki kai-tsaye, domin gujewa miyagun masu jigilar buhunan da ke sanadiyyar tashin farashi.

Shugaban kasar ya yi kira ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu da su nemo dabarar samun kudin kasar waje. Ya ce: “Ku nemo kudinku, ku yi takara da manomanmu.”

Dazu kun ji cewa wani malami a Kano, ya koka game da irin mawuyacin halin da ake ciki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel