Mutanen Arewa da Mahauta za su marawa Gwamna Godwin Obaseki baya a Edo

Mutanen Arewa da Mahauta za su marawa Gwamna Godwin Obaseki baya a Edo

- PDP ta samu goyon bayan Hausawa da sauran ‘Yan Arewa a zaben Edo

- Musulmai da Mahauta duk sun ce za su marawa tazarcen Obaseki baya

- Hakan na zuwa ne bayan Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga garin Benin

Wasu gungun mutanen Arewa da ke zaune a jihar Edo sun tabbatar da goyon bayansu ga tazarcen mai girma Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP.

Sakataren mai girma Sarkin Hausawan Benin, Mohammed Baba, ya bayyana cewa kuri’arsu ta na wurin PDP a zaben gwamnan da za ayi a jihar Edo.

Jaridar Vanguard ta ce wadannan Hausawa da ke zaune a garin Benin sun ce, “Ba mu da zabi illa mu goyi bayan PDP a zaben 19 ga watan Satumban 2020.”

KU KARANTA: Kwankwaso ya dura jihar Edo domin ganin nasarar Obaseki

“Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, Jakadanmu ne. Ya fada mana mu zabi Gwamna Obaseki, kuma hakan za mu yi.” Inji Mohammed Baba.

Game da wannan ra’ayi, sakataren shugaban Hausawan ya bayyana cewa su na daukar Sanata Kwankwaso a matsayin Jagorarsu, kuma su na girmama shi.

Haka zalika wasu Musulmai a karkashin tafiyar “Edo Muslims for Peace and Unity” sun bayyana cewa za su kadawa Godwin Obaseki da Philip Shaibu kuri’arsu.

Kungiyar Edo Muslims for Peace and Unity ta zauna da wasu masu fada-a ji na jam’iyyar PDP na jihar Edo ne a garin Auchi, an yi wannan ganawa ne a jiya.

KU KARANTA: Wani Malami ya ce Musulmai su na cikin tsanani a Najeriya

Shugaban wannan kungiya da sakatarensa, Usman Abbas da Zakawanu Egele sun fitar da jawabi, su ka ce za su goyi bayan PDP ganin rawar da Obaseki ya taka.

Su kuma mahautan jihar Edo sun rufe kwatar dabbobi da duk wasu wuraren saida nama a ranar Alhamis, domin nunawa gwamna Godwin Obaseki goyon baya.

Masu harkar nama a Benin a karkashin Paul Odigie, sun fito kan titi da shanu su na ihun ‘4 + 4’ da ‘Togba’ da nufin cewa gwamna mai-ci Obaseki zai zarce.

A jiya kun ji cewa jigon jam’iyyar PDP, Rabiu Musa Kwankwaso ya na kokarin jawo ra’ayin mutanen Arewa domin su zabi Godwin Obaseki a zabe mai zuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel