Za a riƙa yi wa ‘Yan fyaɗe dandaƙar mazaƙuta a Kaduna inji ‘Yan Majalisar dokoki

Za a riƙa yi wa ‘Yan fyaɗe dandaƙar mazaƙuta a Kaduna inji ‘Yan Majalisar dokoki

- Majalisar dokoki ta yi na’am da yi wa masu fyaɗe dandaƙa a Kaduna

- ‘Yan Majalisar sun yi wa dokokin fyaɗe garambawul ne a zaman jiya

- Kwanakin baya Gwamnatin Kaduna ta nuna ta na goyon bayan haka

A ranar Larabar nan da ta gabata ne Majalisa dokoki ta jihar Kaduna ta amince da yi wa wadanda aka kama da laifin fyade, dandakar mazakuta.

Hakan na zuwa ne bayan ‘yan majalisar jihar sun zauna, sun yi kwaskwarima a kan dokokin fyade.

Majalisar dokoki ta yi garambawul a dokar final kwad na shekarar 2017 na jihar Kaduna, wanda hakan ya bada damar shigo da hukuncin dandaka.

Majalisar jihar Kaduna ta bada wannan sanarwa ne a shafinta na sada zumunta na Twitter. Majalisar ta sanar da wannan ne a jiya Alhamis.

KU KARANTA: Anya: El-Rufai ya ce na kashe N400, 000 wajen dawainiyar mai COVID-19

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, ‘yan majalisar dokokin sun ci ma wannan matsaya ne a zaman da aka yi na ranar Laraba, 9 ga watan Satumba, 2020.

“Wannan doka ta bada shawarar a rika yi wa duk wanda aka samu da laifin fyade dandaka a jihar Kaduna.” Majalisar ta rubuta wannan a shafin Twitter.

Daga baya majalisar ta goge wannan magana da ta yi, amma Jaridar The Cable ta ce shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar ya tabbatar da hakan.

Shugaban masu rinjayen ya yi karin bayani a shafinsa; “Kudirin yi wa dokar final kwad na 5 na jihar Kaduna na shekarar 2017 ya samu karbuwa a majalisa.”

KU KARANTA: CAN ta yi magana game da rikicin Kudancin Kaduna

Za a riƙa yi wa ‘Yan fyaɗe dandaƙar mazaƙuta a Kaduna inji ‘Yan Majalisar dokoki
Majalisar dokokin Jihar Kaduna Hoto: Twitter
Source: Twitter

“Wannan kudiri ya bada damar yi wa masu fyade a jihar (Kaduna) dandakar mazakukuta gaba daya.” Inji babban ‘dan majalisar mai wakiltar Doka da Gabasawa.

A dokar jihar Kaduna, hukuncin daurin shekaru 21 ne ya ke jiran wanda ya yi wa baligi fyade, wanda ya yi lalata da yaro kuwa zai yi zaman kaso har ya mutu.

A baya kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya na goyon bayan a rika cire kayan aikin duk wanda aka samu da laifin yi wa Bayin Allah fyade.

Abin da ba a sani ba shi ne hukuncin da aka tanada ga mata masu irin wannan mugun aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel