Bidiyon dumbin makamai da rundunar soji ta kama bayan kashe Gana
> Rundunar soji ta bayyana yadda ta kashe gagararren dan ta'adda, Terwase Akwaza wanda aka fi sani da Gana
> Ranar Talata, dakarun atisayen AYEM APKATUMA III suka tare tawagar Gana a titin Gbese-Gboko-Makurdi, inda suka kashe shi
> Rundunar ta kuma ce ta cafke yan ta'adda 40 daga cikin tawagar Gana tare da kwato makamai masu yawa a yayin arangamar
Rundunar soji ta yi bajakolin dumbin miyagun makamai da ta samu bayan sun kashe shararren dan ta'adda, Terwaze Akwaza wanda aka fi sani da 'Gana', a jihar Benuwe.
Kafin a kashe shi ranar Talata, an taba saka ladan miliyan N10 a kan duk wanda zai bayar da wata gudunmawa da zata kai ga kama Gana, wanda ya addabi jihohin Benuwe, Nasarawa da Taraba da aikata miyagun laifuka.
Rundunar sojin Nigeria da ke atisayen AYEM APKATUMA III ta bayyana yadda ta kashe gagararren dan ta'addan Benue, Terwase Akwaza wanda aka fi sani da Gana.
Kwamandan rundunar atisayen, Manjo Janar Moundhey Gadzama Ali ya bayyana hakan a daren ranar Talata a karamar hukumar Doma, jihar Nasarawa.
A karamar hukumar ne shelkwatar rundunar soji na musamman guda hudu su ke, kuma a nan ne kwamandan rundunar ya yi holen gawar dan ta'addan Gana.
Manjo Janar Gadzama Ali ya ce: "Na gayya ce ku a daren yau ne domin ku ganewa idanuwanku nasarar da dakarunmu na atisayen AYEM APKATUMA III suka samu.
"Da misalin karfe 12 na ranar Talata, muka samu bayanan sirri na motsin dan ta'addan mai suna Terwase Akwaza Agbadu, da akafi sani da Gana, akan titin Gbese-Gboko-Makurdi.
KARANTA: Miji ya yanke shawarar sakin matarsa bayan gano kwaroron roba 23 a bandaki
KARANTA: 'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a kan kara farashin mai, sun kama 18
"Cikin kwanton bauna dakarun atisayen AYEM APKATUMA III suka ajiye shinge tsaro a titin da misalin karfe 1 na rana, inda suka yi musayar wuta da tawagar dan ta'addan AKA Gana.
"A musayar wutar ne aka kashe shi. A binciken wajen, an gano wadannan makaman; AK 47 guda 5, harsashin FN guda 1, bindigar fistol Beretta guda 2, bindigar PAG guda 3.
"Sauran sun hada da, bindigar maharba guda 1, bindigar Dane guda 10, fistol BP guda 19, fistol FRP guda 35 da kuma bindigar FM guda 2."
Sauran makaman da rundunar ta kwato a cewarsa sun hada da harsasan 7.62mm da harsasan 27.9mm guda 766, sai harsasan AC guda 26.
Ya ce akwai jigida guda 1, kambun tsafi na kugu guda 2, zoben tsafi guda 2 da kuma ababen fashewa guda 2, da ga cikin kayayyakin da rundunar ta kwace.
Ya kuma kara bayyana cewa yan ta'adda 40 daga cikin tawagar Gana na hannun rundunar a yanzu, amma za a mikasu ga rundunar 'yan sanda domin yanke masu hukunci.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng