Hotuna: Kunkuru mai shekaru 80 da mota ta taka ya rayu

Hotuna: Kunkuru mai shekaru 80 da mota ta taka ya rayu

- An samu nasara a aikin da likitoci suka yi wa wani tsohon kunkuru mai shekaru kusan 80 a duniya

- Wata mota ce dai ta taka bayan kunkurun wanda ya yi sanadiyar fashewar bawon bayansa

- Jagoran likitocin ya kuma bayyana cewa za a sake yi wa Kunkurun aiki a nan gaba

Rahotanni sun kawo cewa likitoci sun yi nasarar ceto rayuwar wani kunkuru da ya kai kusan shekaru 80 a duniya.

Likitocin dabbobi a jihar Sokoto ne suka yi wannan namijin kokarin bayan wata mota ta taka kunkurin a farkon makon nan, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Likitocin wadanda suka kai kimanin su shida tare da jami’an jinya sun yi nasarar mayarwa da kunkurun kwanson Bayansa da ya fashe ta sanadiyar hatsarin da ya ritsa dashi a jihar Kebbi.

KU KARANTA KUMA: Na san yadda APC, PDP, da sauransu suke zabar shugabanninsu na kasa, in ji Yari

Hotuna: Kunkuru mai shekaru 80 da mota ta taka ya rayu
Hotuna: Kunkuru mai shekaru 80 da mota ta taka ya rayu Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Shugaban likitocin Dr. Nura Ababukar ya bayyana cewa motar ta taka kunkurun ne a karamar hukumar Argungu da ke jihar Kebbi. Lamarin da ya sa bayan kunkurin fashewa.

Ya ce da farko sun bai wa kunkurun taimakon gaggawa ranar Litinin da daddare, sannan aka yi masa aiki da safiyar Talata.

Dr Nura ya ce: "Abin da muka yi masa shi ne mun hada wajen da zai iya haduwa da danyen bawon bayan na sa, sannan akwai inda ya tararratse da yawa da ba zai gyaru ba, sai muka samu wani abu muka rufe wajen."

Ya ce a yanzu kunkurun da zai cika shekara 80 a watan Fabrairun shekara mai zuwa yana cikin koshin lafiya, kuma za a sake yi masa wani aiki nan gaba.

KU KARANTA KUMA: NSCDC ta kama magidanci kan kashe dan matarsa a jihar Jigawa

Hotuna: Kunkuru mai shekaru 80 da mota ta taka ya rayu
Hotuna: Kunkuru mai shekaru 80 da mota ta taka ya rayu Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

A cewar Dr. Nura kwanson kunkurun kan tallafa masa wurin sarrafa yanayin zafi da kuma taimaka masa wajen yin iyo a ruwa.

A wani labari na daban, mun ji cewa Tinkiya da wasu iyalai suka kiwata a garin Stockport da ke Ingila ta janyo cece-kuce.

An yi gwanjonta inda aka siyar da shi a kan kudi har $490,000 wanda daidai yake da N190,000 miliyan.

Iri tinkiyar mai suna Texel a halin yanzu shine mafi tsada a fadin duniya., shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Tinkiyar mai suna Diamond an siyar da ita a makon nan bayan Charlie Boden da iyalansa sun yi kiwonta a gonarsu ta Mellor Hall.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel