Rabiu Kwankwaso ya isa Benin, ya na ganawa da manyan PDP kan zaben Edo
- PDP ta tura tsohon Gwamnan Kano zuwa Jihar Edo inda ake shirin zabe
- Rabiu Kwankwaso zai taimakawa PDP wajen ganin ta yi nasara a zaben
- Dr. Abdullahi Ganduje shi ne Sarkin yakin jam’iyyar APC a zaben jihar Edo
A jiya ranar Laraba, 9 ga watan Satumba, 2020, mu ka samu labari cewa jam’iyyar PDP ta aika Rabiu Musa Kwankwaso domin aiki na musamman a jihar Edo.
Bisa dukkan alamu, tsohon gwamnan na jihar Kano zai yi wa jam’iyyar PDP kokari wajen ganin ta lashe zaben gwamna da za ayi a ranar 19 ga watan Satumba.
Bayan isar Rabiu Kwankwaso babban birnin Edo, ya karbi ziyarar wasu abokan aikinsa a siyasa.
KU KARANTA: Obaseki da PDP su na rasa wasu manyan kusoshi gabanin zabe
Kamar yadda hadiminsa, Saifullahi Mohammed ya bayyana, mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Edo, Omoagbon Ezekiel ya kai wa Kwankwaso ziyara a jiya.
Cif Omoagbon Ezekiel da tawagarsa ta jagororin jam’iyyar PDP mai mulki a Edo, sun gana da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne a masaukinsa da ke Benin.
A yau ne kuma mai girma mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamred Philip Shu’aibu ya hadu da tsohon Sanatan, kuma babban jigo a jam’iyyar PDP a Najeriya.
Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso sun tattauna da sauran kusoshin PDP na jihar Edo a game da hanyar da za a bi wajen samun nasara a zaben gwamna mai zuwa.
KU KARANTA: PDP da APC za su goge raini wajen lashe kujerun Majalisar dattawa
Wannan ziyara ta zo a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa su ke kokarin karkare yakin neman zabe. Nan da kwanaki tara ne PDP da APC za su kara a akwatin zabe.
Legit.ng Hausa ta samu labari cewa Rabiu Kwankwaso da tawagarsa sun fita yau Alhamis, inda za ayi zama na musamman game da abin da ya kawo sa wannan jiha.
Gwamna Godwin Obaseki wanda yanzu ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP, zai gwabza ne da Osagie Ize-Iyamu, wanda shi kuma wannan karo ya ke takara a APC.
Idan ba ku manta ba gwamna Abdullahi Umar Ganduje, abokin hamayyar Rabiu Kwankwaso a gida, shi ne shugaban kwamitin yakin neman zaben APC a jihar Edo.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng