NSCDC ta kama magidanci kan kashe dan matarsa a jihar Jigawa

NSCDC ta kama magidanci kan kashe dan matarsa a jihar Jigawa

Rundunar tsaro ta Sibil Defens (NSCDC) a jihar Jigawa ta kama wani magidanci mai shekaru 40 da aka ambata da suna Usman Isma’il, bisa zargin kashe dan matarsa mai watanni 17, Adamu Gambo, a karamar hukumar Miga da ke jihar.

Kakakin hukumar NSCDC a jihar, SC Adamu Shehu, ya tabbatar da faruwar al’amarin ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Dutse a ranar Alhamis.

Shehu ya bayyana cewa jami’an hukumar NSCDC sun kama wanda ake zargin, mazaunin kauyen Tsakuwama a ranar 3 ga watan Satumba, da misalin karfe 4:00 na rana.

Ya yi bayanin cewa wanda ake zargin ya dauki marigayin zuwa gona a ranar 14 ga watan Agusta sannan ya murkushe shi har lahira.

Jami’an Sibil Defens a Miga sun kama wani Usman Sama’ila na unguwar Duja, kauyen Tsakuwama, karamar hukumar Miga kan zargin kashe dan matarsa mai watanni 17.

KU KARANTA KUMA: Na san yadda APC, PDP, da sauransu suke zabar shugabanninsu na kasa, in ji Yari

NSCDC ta kama magidanci kan kashe dan matarsa a jihar Jigawa
NSCDC ta kama magidanci kan kashe dan matarsa a jihar Jigawa Hoto: Punch
Asali: UGC

“An kama wanda ake zargin a ranar 3 ga watan Satumba, da misalin karfe 4:00, yayinda lamarin ya afku a ranar 14 ga watan Agusta, inda wanda ake zargin ya dauki marigayin da aka ambata da suna Adamu Gambo zuwa gona sannan ya murkushe shi har lahira.

“Mai laifin ya yi kokarin binne ta’asarsa ta hanyar alkanta mutuwar yaron da ciwon sanyi.

“Sai dai, matarsa ta yi zargin wani abu, a cewarta mijin nata ya yi kokarin murkushe yaron kusan sau biyu, wanda na biyun a kan idonta ne, saboda tsanar da ya yi wa yaron, amma bai cimma nasara ba.

“Sannan bayan yi masa tambayoyi sosai daga hukumar bincike na rundunar, wanda ake zargin ya amsa cewa ya aikata laifin, cewa yaran ya hana matarsa ta bashi kulawa da soyayyar da yake bukata,” ya yi bayani.

A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta damke wani mutum mai shekaru 40 a duniya mai suna Olanrewaju Adeyinka a kan zarginsa da ake da kashe dan uwan shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: An dakatar da shugaban jam'iyyar APC

Ya zargi dan uwan nashi mai suna Gabriel da kawo Aku masu rai guda biyu cikin gidansu da ke yankin Ilaro ta jihar. Hakan yasa kuwa ya soke shi da makami wanda yayi ajalin shi.

Kamar yadda manema labarai suka bayyana, an damke Olanrewaju ne a ranar 12 ga watan Maris kuma ya amsa laifinshi amma ya ce kuskure ne kuma aikin shaidan ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel