Yanzu yanzu: An dakatar da shugaban jam'iyyar APC

Yanzu yanzu: An dakatar da shugaban jam'iyyar APC

- Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar APC kan shugabanci

- Jam’iyyar ta dakatar da shugabanta na jihar Jigawa, Habibu Sara sannan ta nada Muhd Umar domin ya ci gaba da jagoranci

- Dakatarwar da aka yi wa Sara na zuwa ne bayan wani taro na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar reshen jihar

Sabon rikicin shugabanci ya kunno kai a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Jigawa yayinda jam’iyyar mai mulki ta dakatar da Habibu Sara, shugabanta a jihar har sai baba ya gani.

A cewar jaridar The Nation, an dakatar da Sara ne a ranar Laraba, 9 ga watan Satumba, bayan wani taro na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar reshen jihar wanda aka gudanar a gidan gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Jihar Bauchi: Wani babban jigo a PDP ya koma APC, ya bi sahun Dogara

Koda dai APC bata bayyana dalilin dakatar da Shugaban ba, wata majiya a cikin jam’iyyar ta ce matakin na da nasaba da zaben 2023.

An nada Muhd Umar, sakataren jam’iyyar domin ya ci gaba da jagoranci har zuwa lokacin da APC za ta dauki mataki na gaba.

Yanzu yanzu: An dakatar da shugaban jam'iyyar APC
Yanzu yanzu: An dakatar da shugaban jam'iyyar APC Hoto: Track NewsNG
Source: UGC

Dakataccen Shugaban da yake magana da jaridar ta wayar tarho, ya ce dakatarwarsa nufi ne na Allah.

Sara ya ce zai ci gaba da kasancewa mai biyayya ga jam’iyyar, inda ya kara da cewa a shirye yake ya yi duk wani abu da bai take doka ba domin ganin ci gaban APC.

KU KARANTA KUMA: Zan dauki kaddara idan na sha kaye a zabe na gaskiya - Obaseki

Dakatarwarsa na zuwa ne yan kwanaki kadan bayan an dakatar da Daniel Nwafor, shugaban wani bangare na jam’iyyar mai mulki da ta balle a jihar Imo.

An dakatar da Nwafor, wanda ya kasance shugaban jam’iyyar APC da tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha ya sani a Imo, saboda zargin rashin da’a.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi da Marcellinus Nlemigbo, wanda ya kasance wani shugaba ya saki ga manema labarai a ranar Lahadi, 6 ga watan Satumba, a Owerri.

Ya ce an dakatar da Nwafor ne saboda kin bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel