Jihar Bauchi: Wani babban jigo a PDP ya koma APC, ya bi sahun Dogara

Jihar Bauchi: Wani babban jigo a PDP ya koma APC, ya bi sahun Dogara

- Jam’iyyar PDP ta sake rasa wani babban dan siyasa, Salisu Ningi, ga APC a jihar Benue

- Ningi, tsohon dan majalisar wakilai ya kasance na hannun daman Dogara wanda ya bar PDP kwanaki ya koma APC

- Tsohon dan majalisar ya ce ya bar PDP ne saboda ba zai iya ci gaba da kallon gazawarta ba

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sake rasa wani babban jigonta yayinda tsohon dan majalisar wakilai, Salisu Ningi ya sauya sheka daga jam’iyyar a jihar Bauchi.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Ninji ya hade da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, wanda ya bayyana a matsayin jagoransa a bangaren siyasa.

A kwanakin baya ne Dogara ya sauya sheka daga PDP sannan ya koma jam’iyyar APC mai mulki, lamarin da ya zo wa mutane a bazata har ya haifar da cece-kuce.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta kama yan gida daya su hudu da wasu uku kan damfarar yanar gizo

Legit.ng ta tattaro cewa Ningi wanda ya wakilci mazabar Ningi/Warji ya bayyana hakan ta wata wasikar murabus zuwa ga Shugaban PDP na unguwar Ningi.

Jihar Bauchi: Wani babban jigo a PDP ya koma APC, ya bi sahun Dogara
Jihar Bauchi: Wani babban jigo a PDP ya koma APC, ya bi sahun Dogara Hoto: Ondo APC
Asali: UGC

Ya ce yanayin jam’iyyar ta fice masa daga rai kuma cewa ba zai yarda a ci gaba da alakanta shi da magoya bayansa da “gazawar PDP ba.”

“Ka tuna cewa, a lokacin zaben 2019, manyan yan siyasa daga jihata, Bauchi karkashin jagorancin ubangidana, Mai girma Rt. Hon. Yakubu Dogara sun sauya sheka zuwa PDP domin hambarar da mumunar gwamnati ta M.A. Abubakar kuma suka yi nasarar daura Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, amma da tafiya ta yi tafiya, sai na gano cewa ba a magance matsalar da ta sa muka hade domin ceto jiharmu ba,” ya rubuta.

KU KARANTA KUMA: Zan dauki kaddara idan na sha kaye a zabe na gaskiya - Obaseki

A wani labari na daban, mun ji a baya cewa Gwamnan jihar Bauchi, Bala AbdulKadir Mohammed, ya siffanta tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, da ya sauya sheka zuwa All Progressives Congress APC a matsayin annoba a siyasa.

Ya zargi Dogara da kara kudi a kwangila a ayyukan da yakeyi a mazabarsa.

Ya bayyana hakan ne yayinda daruruwan masoya daga kananan hukumomin Dass, Tafawa Balewa da Bogoro, da Yakubu Dogara ke wakilta suka kai masa ziyara gidan gwamnati ranar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel