An fara musayar yawu tsakanin Oshiomole da matar mataimakin gwamnan Edo

An fara musayar yawu tsakanin Oshiomole da matar mataimakin gwamnan Edo

- Oshiomhole ya yi watsi da zargin da matar mataimakin gwamnan Edo, Maryam Shaibu ke yi masa

- Misis Shaibu ta yi zargi a cikin wani rubutaccen korafi cewa tsohon shugaban na APC ne tushen barazanar da ake yi mata

- Sai dai Oshiomhole ya karyata zargin, yana mai cewa shi mutum ne mai son zaman lafiya

Tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, Adams Oshiomhole, ya yi martani a kan zargin da Maryam Shaibu, matar mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ke masa.

Matar mataimakin gwamnan ta yi zargin cewa Oshiomhole ne tushen barazana da ake yi mata da iyalinta.

Misis Shaibu a cikin wani rubutaccen korafi ta hannun lauyanta, Idemudia Ilueminosen & co, zuwa ga kwamishinan yan sandan jihar Edo, Johnson Kokumo, ta yi ikirarin cewa Oshiomhole ya kaddamar da cewa ya aika wasu yan daba.

Cewa yan daban su dunga lura da shige da ficen ta a karamar hukumar Etsako ta yamma domin su lallasa ta.

KU KARANTA KUMA: Yafewa masu laifi: Gwamnan Bauchi ya gane kuskuren sa, ya roki afuwa

An fara musayar yawu tsakanin Oshiomole da matar mataimakin gwamnan Edo
An fara musayar yawu tsakanin Oshiomole da matar mataimakin gwamnan Edo Hoto: This Day
Asali: Depositphotos

Sai dai da yake martani kan lamarin tab akin hadimin labaransa, Victor Oshioke, Oshiomhole ya yi watsi da karar matar Shuaibu.

Ya ce tana kokarin karkatar da hankalin mutane daga bidiyonta da ke yawo inda take barazanar yi wa mata duka idan suka halarci kowani taro baya ga wanda ta shirya, jaridar The Nation ta ruwaito.

“Korafin wani yunkuri ne na bata sunan Kwamrad Oshiomhole. Shaibu da matarsa su nemi wata hanyar na gyara sunan gidansu, wanda ya riga ya baci ta sanadiyar yin wasu zantuka da bai kamata ba, wanda aka dauka a bidiyo, suna barazanar tashin hankali a kan mutanen Edo.

“Kwamrad Oshiomhole ya kasance mutum mai son zaman lafiya. Ya mayar da hankali wajen tallata wa mutanen Edo dan takarar jam’iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu, da ajandarsa ga mutanen Edo, domin amfaninsu.

KU KARANTA KUMA: Rashawa: Gwamna Sule zai yi sauye-sauye a majalisar zartarwa ta jihar Nasarawa

“Kananan kwari irin su Saibu da matarsa ba za su taba iya janye hankalin Oshiomhole daga aikin gabansa ba,” in ji Oshioke.

A gefe guda, Gwamna Godwin Obaseki ya bayyana cewa zai dauki kaddara idan har ya sha kaye a zabe na gaskiya da adalci.

Obaseki ya bayyana hakan ne a yayinda ya zanta da manema labarai bayan ya ziyarci sufeto janar na yan sanda, Mohammed Adamu a hedkwatar rundunar da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel