2023: Kusoshin APC guda 3 sun shirya kwace Adamawa daga hannun PDP

2023: Kusoshin APC guda 3 sun shirya kwace Adamawa daga hannun PDP

- Jam’iyyar APC na gudanar da wani gagarumin shiri don kwace jihar Adamawa a 2023

- Gwamna Ahmad Fintiri na PDP ya kayar da tsohon gwamnan jihar, Jibrilla Bindow, a 2019 saboda wani rikicin cikin gida da aka kasa magancewa a APC

- An tattaro cewa Boss Mustapha, babban sakataren gwamnatin tarayya na jagoranta kokarin da suke na kwato jihar daga hannun PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai mulki a jihar Adamawa na iya fuskantar kalubale wajen zarcewa a jihar a 2023 idan har shirin siyasa da shugabannin All Progressives Congress (APC) ke yi ya cimma nasara.

Legit.ng ta runa cewa APC ta rasa jihar a 2019 sakamakon wani rikici da aka kasa sasantawa tsakanin tsohon gwamnan jihar, ibrilla Bindow, da wasu shugabannin jam’iyyar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wasu yan asalin jihar da ake ganin mutuncinsu na aiki don hanin sun kwato jihar a zabe na gaba.

Wadannan mutane kuwa sune babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da tsohon SSG, David Babachir.

2023: Kusoshin APC guda 3 sun shirya kwace Adamawa daga hannun PDP
2023: Kusoshin APC guda 3 sun shirya kwace Adamawa daga hannun PDP Hoto: Boss Mustapha
Source: Twitter

An tattaro cewa Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar EFCC, tsohon gwamna Bindow, da surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ahmed Halilu (Mudi), na aiki sosai don dawo da APC a jihar.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Obaseki na kara shiga matsala yayinda jiga-jigan PDP ke komawa APC

Rahoton ya kuma bayyana cewa “Sanata mai wakiltan yankin Adamawa ta tsakiya a majalisar dokokin tarayya, wani mamba mai wakiltan Jada/Ganye/Mayo-Belwa/Toungo a majalisar wakilai, Abdulrazak Namdas, da tsohon mataimakin gwamnan jihar, Babale Martins” na cikin shirin jam’iyyar na kwato jihar a 2023.

Tsohon gwamnan jihar Bindow ya sha kaye a hannun dan takarar jam’iyyar PDP, Ahmadu Fintiri a zaben 2019.

A wani labarin kuma, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Adamawa, Bala James Ngilari, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen mutane 18 da suka shiga sahun masu kudin duniya a 2020

Da yake bayar da dalilansa na sauya sheka, Ngilari ya yi korafin cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar ba ta yi masa adalci.

Ya ce bada dadewa ba za a fitar da jawabin sauya shekarsa, inda ya kara da cewa wasu jiga-jigan PDP da dubban magoya bayansu za su same shi a APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel