UN ta na so a tabbatar da kariyar ‘Yan makaranta da malamai kafin a koma aji

UN ta na so a tabbatar da kariyar ‘Yan makaranta da malamai kafin a koma aji

- Majalisar dinkin Duniya ta aikawa gwamnati gargadi kan batun bude Makarantu

- Wani jami’in majalisar ya ce dole a tabbatar da kare mutane kafin a koma karatu

- A cewar UN, dalibai da sauran masu ruwa da tsaki za su fu samun natsuwar aiki

Majalisar dinkin Duniya ta bukaci gwmnatin Najeriya ta kare yaran makaranta da malamai daga hare-haren miyagu yayin da ake maganar sake bude makarantu.

A lokacin da ake tunanin yadda za a dawo karantar da yara a Najeriya, wani babban jami’in UN, Edward Kallon, ya yi kira ga gwamnati ta tabbatar za ta kare jama’a.

Edward Kallon ya yi wannan kira ne a ranar Talata, 8 ga watan Satumba, 2020 domin tuna ranar kare ilmi ta Duniya wanda aka soma gudanarwa a shekarar bana.

Kallon wanda ke jagorantar taimakon agaji da gaggawan majalisar Duniyar ya ce za a fi samun karfin komawa karatu idan gwamnati ta yi alkawarin kare ran jama'a.

KU KARANTA: Najeriya ta fara maganar bude makaranta bayan hutun COVID-19

Yanzu ma’aikatar ilmi ta rufe duk wasu makarantu saboda rage yaduwar cutar COVID-19, amma kafin wannan annobar ta shigo, ana fama da rashin tsaro a yankin Arewa.

Kallon ya ce: “A lokacin da gwamnatocin jihohi su ke tunanin bude makarantu bayan tsawon lokaci su na rufe, ya kamata shiryawa yiwuwar aukuwar wani mummunan abu ya zama cikin tanadin annobar da ake yi.”

Jami’in ya kara da cewa: “Ilmi ya na da matukar muhimmanci wajen taimakawa mutanen Arewa maso yammacin kasar da aka jikkata wajen sake ginasu da tadosu.

Ya ce: “Hari ga makarantu, hari ne kai-tsaye ga al’ummomin da za ayi nan gaba. Ina kira ga duk masu ta-cewa a rikicin, su dauki duk matakan da su ka dace na tsare karatu da ba yara ilmin da za su yi takama gobe.

KU KARANTA: Za ayi fama da karancin isasshen abinci a Garuruwa saboda COVID-19

UN ta na so a tabbatar da kariyar ‘Yan makaranta da malamai kafin a koma aji
‘Yan makaranta a Najeriya Hoto: Legit
Asali: UGC

Majalisar ta ce maida hankali ga kare lafiya da rayukan malamai da daliban ilmi shi ne hanyar da za a bi wajen tsare jarin da gwamnati ta zuba a harkar ilmi a yankin.

Kallon ya yi kiran hadin-kai wajen samu a shawo kan ta’addanci a Najeriya, ya na mai tabbatar da cewa ‘yan ta’adda sun tarwatsa karatun bokon miliyoyin yara a kasar.

‘Yan ta’addan Boko Haram sun tada garuruwa da dama a bangaren Arewa maso gabas. A yanzu gwamnatin shugaba Buhari ta na kokarin ganin komai ya dawo daidai.

A wani gefe guda kuma, ana fama da annobar COVID-19 a fadin Najeriya da ma wasu kasashen.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel