Ministoci su gabatar da bukatar ganina wajen SGF ko shugaban Ma’aikatan fada inji Buhari

Ministoci su gabatar da bukatar ganina wajen SGF ko shugaban Ma’aikatan fada inji Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake fadawa ministocin gwamnatinsa da su gabatar da bukatar ganinsa zuwa ofishin babban hadiminsa.

Tun 2015 ne shugaban Najeriyar ya ba ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa karfi, ta yadda duk wata takardar ganinsa sai ta bi ta karkashinsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada wannan umarni ne a lokacin da ya ke magana wajen taron cikar ministocin Najeriya shekara guda a kan mukamansu

Yayin da ministocin su ka cika shekara a gwamnati, shugaba Buhari ya kira taro na musamman inda ya duba aikin da manyan mukarraban na sa su ke yi.

KU KARANTA: Ministan jiragen sama ya yi gwajin cutar COVID-19 sau 10 a cikin watanni 6

A wajen wannan taro da aka yi a cikin fadar shugaban kasa, Buhari ya kara jaddada umarnin da ya bada a lokacin da ya fara nada wadannan ministoci a 2019.

“Bari in sake jaddada cewa duk wata takarda da ake bukatar in duba ko kuma neman ganawa da ni ta bi ta karkashin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa."

Shugaba Buhari ya kara da cewa: “Haka zalika duk wasu harkokin majalisar zartarwa ta bi ta karkashin sakataren gwamnatin tarayya.”

Shugaban Ma’aikatan fadar Shugaban kasa da SGF
Shugaban Ma’aikatan fadar Shugaban kasa da SGF Hoto: Twitter/NGRPresident
Source: Twitter

Wajen ganin shugaban kasa ido-da-ido, minista zai tuntubi Farfesa Ibrahim Gambari, wanda ya maye gurbin Marigayi Abba Kyari kwanakin baya.

Da wannan umarni da mai girma Muhammadu Buhari ya jaddada, duk wata takarda ta ofishin minista ko sha’anin majalisar ministoci sai ta je gaban Boss Mustapha.

KU KARANTA: CNCE ta roki Shugaban kasa Buhari ya tsige Shugabannin tsaro

Jaridar The Cable ta ce wannan ne karo na biyu da shugaban kasar ya fadawa jerin ministoci masu-ci wannan. Wasu daga cikin ministocin sun san da wannan doka tun 2015.

A lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya fara bada wannan umarni, wasu sun yi ta ganin cewa an ba shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar ikon da ya yi yawa.

Da wannan mataki da shugaban Najeriyan ya tabbatar a yanzu, ya nuna cewa haka salon mulkinsa ya ke, akasin kallon da wasu su ka rika yi wa Marigayi Malam Kyari.

Idan za ku tuna a watan Afrilu ne Abba Kyari ya rasu, sakamakon kamuwa da cutar COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel