Tsohon gwamnan jihar Adamawa ya sauya sheka zuwa APC, ya ce PDP ba ta yi masa adalci

Tsohon gwamnan jihar Adamawa ya sauya sheka zuwa APC, ya ce PDP ba ta yi masa adalci

- Mista Bala James Ngilari ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC)

- Ngilari ya kasance tsohon gwamnan jihar Adamawa

- Tsohon gwamnan ya yi korafin cewa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP ba ta yi masa adalci

Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Bala James Ngilari, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Da yake bayar da dalilansa na sauya sheka, Ngilari ya yi korafin cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar ba ta yi masa adalci.

Ya ce bada dadewa ba za a fitar da jawabin sauya shekarsa, inda ya kara da cewa wasu jiga-jigan PDP da dubban magoya bayansu za su same shi a APC.

KU KARANTA KUMA: An caccaki Buhari da iyalansa kan karya dokokin CBN da NCDC a bikin Hanan

Tsohon gwamnan jihar Adamawa ya sauya sheka zuwa APC, ya ce PDP ba ta yi masa adalci
Tsohon gwamnan jihar Adamawa ya sauya sheka zuwa APC, ya ce PDP ba ta yi masa adalci Hoto: Nta.ng
Source: Facebook

“Zai fi mani na koma APC inda za a ga kimana sannan a so ni saboda PDP a Adamawa ba ta mani adalci, dole na zama dan takara.

“Kwanan nan za a shirya taron manema labarai inda ni da magoya bayana za mu sauya sheka ciki harda manyan yan PDP,” Ngilari ya sanar da jaridar Tribune.

KU KARANTA KUMA: Karin farashin man fetur: Yan sanda sun ce ba za su bari ayi zanga-zanga ba a jihar Borno

A wani labarin kuma, tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara yayin mulkin tsohon gwamna Abdulaziz Yari, Sanda Danjari, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai mulki a jihar.

Danjari, wanda ya bar jam'iyyar APC, ya samu tarbar arziki a ranar Laraba daga wurin Gwamna Bello Matawalle a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.

Kamar yadda yace, yanayin kwazon gwamnan da salon mulkinsa ya ja shi komawa tafiyarsa, jaridar Daily Nigerian ta wallafa.

Ya jinjinawa gwamnan a fannin tsaro da shugabanci nagari, wanda yace hakan suna daga cikin dalilan komawarsa jam'iyyar PDP.

Tsohon kwamishinan ya yi kira ga gwamnan da kada yayi kasa a guiwa wurin samar da tsaro tare da shugabanci nagari a jihar.

Ya tabbatar da bada gudumawarsa wurin ganin ci gaban jam'iyyar a jihar.

A jawabinsa, shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Ibrahim Mallaha, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Hassan Damri, ya ce za su ci gaba da tabbatar da goyon bayansu ga jam'iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel