Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo zai jagoranci kungiyar ECOWAS
Gwamnatin kasar Ghana ta bada sanarwar cewa an zabi shugaba Nana Akufo-Addo a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS.
Mai girma Mista Nana Akufo-Addo zai jagoranci wannan kungiya ta kasashen yammacin Nahiyar Afrika na tsawon wa’adi guda.
An zabi Nana Akufo-Addo mai shekara 76 a matsayin sabon shugaban ECOWAS ne a taron da ake yi a Niamey, Jamhuriyar Nijar.
Yanzu haka mafi yawan shugabannin Afrika ta yamma su na kasar Nijar inda ake gudanar da taron kungiyar ECOWAS na 57.
KU KARANTA: Najeriya ta na cikin kasar da ta fi kowace arahar kudin fetur
Jaridar Premium Times ta ce ana wannan zama ne a babban dakin taro na Mahatma Gandhi da ke kasar Nijar.
Shugabannin yankins su na tattaunawa a kan wani zama da majalisar tsaro ta kungiyar ECOWAS ta yi kafin wannan taro mai-ci.
Bayan an zabi sabon wanda zai jagoranci ECOWAS, Nana Akufo-Addo ya tabbatar da wannan nauyi da aka daura masa a jiya.
An zabi Akufo-Addo ne ba tare da hamayya ba domin shi kadai ne wanda ya tsaya takarar neman wannan kujera.
KU KARANTA: COVID-19 za ta iya jawo cututtuka masu hadari su kama Yaran Afika
Nana Akufo-Addo ya rubuta: “A ranar Litinin, 7 ga watan Satumba, 2020, shugabannin kasashe da kungiyar ECOWAS su ka dauki matakin zabena ba tare da hamayya ba a matsayin shugaban ECOWAS na tsawon wa’adi guda na shekara daya.”
A jawabin da sabon shugaban na ECOWAS ya yi a shafinsa na Twitter, ya ce hadin-kan Afrika zai jawowa kowace kasa cigaba.
“Ina kira ga sauran takwarorina su bada gudumuwarsu wajen matakan da za mu dauka, tare da kawowa yankunanmu cigaba.”
Ya ce: “Mutanenmu babu abin da su ke bukata da ya gaza wannan. Da haka za a cinma manufofin ECOWAS na zaman lafiya, cigaba da nasara.”
A baya kun ji cewa sauran abubuwan da shugabannin za su tattauna a kai sun hada da rikicin siyasar kasar Mali da COVID-19.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng