Abin ya isa, ya kamata a fatattaki Hafsun Sojojin da su ka gaza inji Kungiyar CNCE

Abin ya isa, ya kamata a fatattaki Hafsun Sojojin da su ka gaza inji Kungiyar CNCE

Ganin yadda ake fama da matsalar rashin tsaro har gobe, wata kungiya mai suna CNCE ta manyan Arewa, ta yi kira ga shugaban kasa ya sauya hafsun sojoji.

Kungiyar CNCE ta dattawan Arewa maso tsakiyar Najeriya ta na ganin sauke shugabannin sojoji shi ne zai taimaka wajen ganin an samu tsaro da cikakken zaman lafiya.

Jaridar Vanguard ta ce wannan bayani ya fito ne a wani jawabi daga bakin shugaban kungiyar CNCE, Usman Bida da sakatarensa, Moses Okudu, jiya a garin Abuja.

Kungiyar ta fito ta yi wannan magana ne bayan da jami’an kwastam su ka sanar da hukumomi cewa ana zargin ‘yan ta’addan Boko Haram sun shigo yankin Abuja.

KU KARANTA: Likitoci za su tafi yajin-aiki, sun fara zuga sauran Malaman asibiti

“Mu na tare da sauran ‘Yan Najeriya, mu na kiran shugaban kasa ya yi maza ya canzawa hukumomin tsaro zani ta hanyar tsige hafsun sojoji a matsayin matakin farko.”

Kungiyar CNCE ta ce: “’Yan Najeriya sun gaji da gafara sa, ba su ka ga kaho ba a sha’anin tsaro.”

“Mu na takaicin yadda babu wata jiha a tsakiyar Arewa da ba a samun harin ‘yan ta’adda ko kuma a kashe Bayin Allah haka kawai, yankin da a baya ya fi kowane zaman lafiya a Arewa.”

CNCE ta ce jim kadan da samun labarin kama ‘yan ta’adda fiye da 400 da mugayen makamai a Nasarawa, sai kuma ga jita-jitar Boko Haram sun shiga Abuja da kewaye.

KU KARANTA: ‘Yan Kungiyar IPOB sun kai wa Yankin Hausawa farmaki a Ribas

Abin ya isa, ya kamata a fatattaki Hafsun Sojojin da su ka gaza inji Kungiyar CNCE
Shugaban kasa tare da IGP Hoto: Fadar Shugaban Najeriya/Channels
Asali: Facebook

Wannan kungiya ta cigaba da jawabi cewa: "A yau hankalin mutanen Najeriya da wadanda si ke zaune a Arewa maso tsakiya ya tashi da wannan labari”

“Ba a shiga wasu bangarorin Nasarawa, Neja, Kogi saboda ‘yan ta’adda su na kisa, sata, da garkuwa da mutane, sai ka ce mu na zaman dawa.” Inji CNCE.

“Mun zabi shugaba Muhammed Buhari ne saboda kwarewarsa a sha’anin tsaro da gaskiyarsa, kuma mu na sa ran mu ga ya yi kokari.” Kungiyar ta ce mu na tare da shi har gobe.

“Mu na kira ga shugaban kasa, babu yadda za a ce jami’ai hudu sun fi duka dubunnan sojojin da mu ke da su kwarewa, a kan wannan gaba ne mu ke kira ka sauke hafsun da ba su san aiki ba.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel