Ya zama dole a dakatar da wannan haukan – Sultan ya yi magana kan kashe-kashen kudancin Kaduna

Ya zama dole a dakatar da wannan haukan – Sultan ya yi magana kan kashe-kashen kudancin Kaduna

Sa’ad Abubakar III, Sultan na Sokoto, ya yi kira ga kawo karshen kashe-kashe a kudancin Kaduna.

Yankin ta fuskanci yawan hare-hare da ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi.

Da yake magana a taron kungiyar sarakunan arewa a Kaduna a ranar Litinin, 7 ga watan Satumba, basaraken ya bayyana rikicin a matsayin “hauka da ya zama dole a dakatar dashi cikin gaggawa”.

Ya yi kira ga wadanda ke da hannu a kashe-kashen da su daina mummunan aika-aikan, inda ya ce “hakan ya ishe su.”

Sultan ya ce: “babu wani mutum da ke cikin hankalinsa da zai je yana kashe-kashen bayin Allah bisa ko wani hujja.”

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun halaka wani hazikin sojan sama a Kaduna (hoto)

Basaraken ya kuma zargi yan siyasa da rura wutar rikicin, inda ya roki yan Najeriya da kada su bari a mayar da su karen farauta, jaridar The Cable ta ruwaito.

Ya zama dole a dakatar da wannan haukan – Sultan ya yi magana kan kashe-kashen kudancin Kaduna
Ya zama dole a dakatar da wannan haukan – Sultan ya yi magana kan kashe-kashen kudancin Kaduna
Source: UGC

“Idan kuka ci gaba da rura wutar kashe-kashen saboda banbanci kabila ko addini toh bayin Allah ake kashewa yayinda ake kare masu mulki” in ji shi.

Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce rikicin kudancin Kaduna ya samo asali tun rikicin Kasuwan Magani na farko da aka yi a karamar hukumar Kajuru a 1980.

Ya ce gwamnatinsa na ta kokarin ganin ta kawo karshen kashe-kashen da dawo da zaman lafiya.

Gwamnan ya kara da cewa an samar da wani sansanin sojoji da tashar yan sandan tafi da gidanka a yankin yayinda aka tura rundunar tsaron sama yankin.

Ya ce ana amfani da kayayyaki kamar su jirage marasa matuka da na’urar gano lambar waya wajen kashe yan bindiga a jihar.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta kashe yan ta’adda 9, sun ceto mutum 7 a Gwoza

A wani labarin, rundunar Operation Accord sun kashe wasu ‘yan bindiga hudu a yankin Jeka Da Rabi da ke hanyar babbar titin Kaduna-Abuja a jihar Kaduna sannan sun samo makamai daga hannunsu.

Shugaban sashin labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar John Enenche ne ya tabbatar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Alhamis.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel