Sojoji sun kashe yan bindiga 5, sun kuma kama 8 a Nasarawa da Benue

Sojoji sun kashe yan bindiga 5, sun kuma kama 8 a Nasarawa da Benue

- Rundunar sojoji a jihohin Benue da Nasarawa ta kashe yan bindiga biyar yayinda suka kama wasu takwas

- An kashe yan bindiga hudu a yayin wani mamaya da aka kai mabuyarsu a Tse Agi, karamar hukumar Gwer ta yamma a jihar Benue

- An kuma kashe daya daga cikin yan bindigan a lokacin da dakarun suka kai farmaki sansaninsu da ke iyakar Benue-Nasarawa

Rundunar sojoji na Operation Whirl Stroke a jihohin Benue da Nasarawa sun kashe yan bindiga biyar yayinda suka kama wasu takwas.

Jagoran labarai na ayyukan rundunar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya ce an kashe yan bindiga hudu a yayin wani mamaya da aka kai mabuyarsu a Tse Agi, karamar hukumar Gwer ta yamma a jihar Benue.

Ya kuma bayyana cewa an kashe daya daga cikin yan bindigan a lokacin da dakarun suka kai farmaki sansaninsu da ke iyakar Benue-Nasarawa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gidaje, shaguna sun kone kurmus yayinda motar tanka ta kama da wuta a jihar Neja

Sojoji sun kashe yan bindiga 5, sun kuma kama 8 a Nasarawa da Benue
Sojoji sun kashe yan bindiga 5, sun kuma kama 8 a Nasarawa da Benue
Asali: UGC

Eneche wanda ya bayyana cewa an samo alburusai da dama a yayin arangaman, ya yaba ma jama’a a kan bayar da muhimman bayanai na kwararru wanda ya sa aka cimma nasara.

A wani labari mai alaka, Hedkwatar tsaro ta Najeriya ta ce dakarun ta na Operation Thunder Strike sun kashe ƴan bindiga masu yawa a harin da ta kai sansaninsu da ke dajin Kuduru da Kuyambana a jihar Kaduna.

Kakakin rundunar ta musamman, Manjo Janar John Enenche ne ya sanar da hakan ta shafin rundunar na Twitter a ranar Juma'a a Abuja.

Enenche ya ce sojojin sun samu sahihan bayanan sirri da ke nuna yan ta'addan na amfani da wuraren don shirya kai hari kafin aka far musu.

Ya ce an kai harin a maɓuyar ƴan ta'addan a dajin Kuduru ne na'urar leƙen asiri ya nuna akwai ƴan bindiga da dama a cikin gine-ginen da ke dajin.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun halaka wani hazikin sojan sama a Kaduna (hoto)

A cewarsa, rundunar dakarun saman ta NAF ta aike da jiragen yaƙi da jirgi mai saukan ungulu masu ɗauke da bindiga zuwa wurin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel