Kungiyar daliban Najeriya ta aikawa Buhari zazzafan sako a kan karin farashin mai

Kungiyar daliban Najeriya ta aikawa Buhari zazzafan sako a kan karin farashin mai

Kungiyar daliban Najeriya (NANS) ta fadawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya janye karin farashin man fetur da gwamnatinsa ta yi ko kuma dalibai su mamaye titunan Najeriya a wata gagarumar zanga-zanga da bai taba ganin irinta ba.

NANS ta ce ta yi matukar girgiza da jin labarin cewa gwamnati ta sanar da yin karin kudin litar man fetur daga N145 zuwa N161.

A cikin wani jawabi da mataimakin shugaban kungiyar, Kwamred Ojo Raymond, ya fitar, NANS ta bayyana karin farashin man fetur a matsayin almara, tunzura jama'a da kuma nuna zallar rashin tausayi.

"Daliban Najeriya sun yi watsi da karin farashin litar man fetur saboda hakan zai kara tsananin matsin rayuwa, zai shafi harkokin kasuwanci, sannan ya shafi tattalin arzikin mutane da iyali.

"Abin takaicin shine; a cikin sati daya kawai, an samu karin kudin wutar lantarki, farashin man fetur, da sauran wasu abubuwan more rayuwa. 'Yan Najeriya basa farin ciki da hakan, musamman batun karin farashin mai, wanda shine na baya bayan nan," a cewarsa.

Kungiyar daliban Najeriya ta aikawa Buhari zazzafan sako a kan karin farashin mai
Kungiyar daliban Najeriya ta aikawa Buhari zazzafan sako a kan karin farashin mai
Source: Facebook

A makon da ya gabata ne Legit.ng Hausa ta wallafa labarin cewa dubban 'yan Najeriya sun yi tururuwa wajen bayyana ra'ayinsu tare da mayarwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, martani a kan kara farashin man fetur da kuma tsadar kayan abinci.

KARANTA: Da ma can ba a dora Najeriya a kan turbar cigaba ba - Sanusi ya yi magana a kan karin farashin man fetur

KARANTA: Matsin rayuwa: Yadda hotunan kanin gwamna ya na asuwaki da cinyar kaji sun jawo cece-kuce a dandalin sada zumunta

Hauhawar farashin kayan abinci da kara farashin litar man fetur da karin kudin wutar lantarki sun harzuka 'yan Najeriya, lamarin da yasa jama'a da dama ke bayyana nadamarsu tare da yin da na sanin goyon bayan gwamnatin Buhari.

A ranar Laraba, 03 ga watan Satumba, ne kafafen yada labarai su ka wallafa labarin cewa kamfanin tallar man fetur mallakar gwamnatin tarayya (PPMC) ya sanar da kara farashin litar mana fetur zuwa N151 kowacce lita.

Kafin fitowar sanarwar kara farashin man fetur, hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasa (NERC) ta sanar da yin karin kudin wutar lantarki daga N27.2 zuwa N66 a kan kowanne KW a ranar Talata, 1 ga watan Satumba.

Da ya ke martani a kan karin kudin wutar lantarki, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, ya ce ko kadan bai kamata karin kudin ya zo a irin wannan lokaci da jama'a suke a galabaice ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel